Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi

94. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce; “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’aba ya ba mu labari daga Muhammad dan Ziyad ya ce, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunSa, lallai zan kore wasu jama’a daga tafkina […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi

94. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce; “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’aba ya ba mu labari daga Muhammad dan Ziyad ya ce, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunSa, lallai zan kore wasu jama’a daga tafkina kamar yanda ake kore bakin rakuma daga tafki (korama).”
95. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Ayyub da Kasir dan Kasir dayansu yana kari bisa dan uwansa; cewa daga Sa’ad dan Jubair ya ce, “dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Allah Ya jikan Uwar Isma’il! Da dai ta kyale zam-zam, ko ya ce, da ta kamfata daga ruwa da ya kasance korama mai gudana. kabilar Jurhum suka taho suka ce, “shin ko za ki yi mana izinin sauka a wurinki? Ta ce, “Na’am, amma ba ku da wani hakki game da ruwan nan,” suka ce, “Na’am.”  
96. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru daga Abu Salih Samman ya ce daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce, “Mutum uku Allah ba zai yi magana da su ba, kuma ba zai yi dubi gare su ba: (1) Mutumin da yake rantsuwa bisa kayan kasuwanci cewa, lallai ya saya bisa farashin kaza-da-kaza don ya karbi fiye da haka. (2) Da mutumin da ya rantse a bayan La’asar bisa karya domin ya karbe dukiyar wani Musulmi. (3) Da mutumin da ya hana sauran ruwa, Allah zai ce: “Yau zan hana maka sauran ruwaNa kamar yadda ka hana bisa ga abin da hannunka bai aika (halitta) ta komai ba gare shi (ruwa).” Aliyu ya ce, “Sufiyan ya ba mu labari ba sau daya ba, daga Amru cewa, ya ji Abu Salih yana isarwa da shi ga Annabi (SAW).

Babi na Goma Sha Biyu: Babu iyaka (mallakar kasa) face ga Allah da ManzonSa (SAW):    
97. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yunus daga dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbatu daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Sa’ab dan Jassamatu ya ce, “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu mallakar wata kasa face ga Allah da ManzonSa.” Kuma labari ya isa gare mu cewa, “Lallai Annabi (SAW) ya mallaki (iyakance) Naki’u, kuma Umar ya mallaki Sharafa da Rabzat.”

Babi na Goma Sha Uku: Shayar da mutane da dabbobi daga koramu:
98. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik dan Anas ya ba mu labari daga Zaid dan Aslam daga Abu Salih Samman daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Doki ga wani mutum lada ne; ga wani mutum kuma sutura ne; ga wani mutum kuma nauyi ne. Amma wanda ke da lada, shi ne wanda ya daure (doki) a tafarkin Allah, ya tsawaita igiyar dauri ko makiyaya, duk abin da ya samu ta hanyar dauri ko makiyaya na da sakamako mai kyau ko da igiyar ya tsinke bisa kulli daya ko biyu. Gurabbanta da kashinta duk suna da sakamakon mai kyau. Ko da ta shude da korama ta sha daga gare shi, kuma ko ba shi ya kore ta daga mashayar shi ma ya kasance na da sakamako mai kyau, wato yana da lada kan haka. Amma wanda ya daure doki don wadata ko don kamun kai, sa’an nan bai manta da hakkokin Allah bisa wuyansa ko bayansa ba, wannan shi ne (daure doki) ya zamo masa sutura. Amma wanda ya daure doki don alfahari da nuniya ko cutar da jama’ar Musulmi. Wannan shi ne wanda (rikon doki) ya zamo masa nauyi (zunubi).” Kuma an tambayi Manzon Allah (SAW) game da jakuna, sai ya ce: “Ba a saukar mini da komai ba face wan nan aya wadda take kunshe da dukkan komai cewa: “Wanda duk ya aikata wani aiki misalin kwayar zarra na alheri zai gan shi. Kuma wanda ya aikata wani aiki misalin kwayar zarra na sharri zai gan shi (k:99:7-8).”