Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi, Babi na Biyar:
Husuma a cikin rijiya da kara game da ita:86. An karbo daga Abdan ya ce: “Daga Abu Hamza daga A’amashi daga Shakik daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya rantse domin ya amshe dukiyar wani mutum, alhali shi ke kanta bisa fajirci, zai hadu da Allah Yana fushi […]
Husuma a cikin rijiya da kara game da ita:
86. An karbo daga Abdan ya ce: “Daga Abu Hamza daga A’amashi daga Shakik daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya rantse domin ya amshe dukiyar wani mutum, alhali shi ke kanta bisa fajirci, zai hadu da Allah Yana fushi da shi.” Sai Allah Madaukaki Ya saukar da cewa: “Wadannan da suke sayen alkawarin Allah da rantsuwoyinsu bisa ’yan tamanni kadan… har karshen aya (k:3:77).” Sai Asha’as ya zo ya ce: “Abin da Abdurrahman ya ba ku labari wannan aya ta sauka ne bisa kaina, sai (Annabi) ya ce, mini: Kawo shaidarka,” na ce, “Ba ni da shaida,” ya ce, “To sai rantsuwarsa,” na ce, “Ya Manzon Allah! To ya rantse.” Sai Annabi (SAW) ya ambaci wannan labari, sai Allah Ya saukar da wannan domin gaskata shi.”
Babi na Shida:
Laifin wanda ya hana matafiyi ruwa:
87. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdulwahid dan Ziyad ya ba mu labari daga A’amashi ya ce, “Na ji Abu Salih yana cewa, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Mutum uku Allah bai dubansu Ranar kiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da wata azaba mai radadi. (1) Mutumin da ke da sauran ruwa bisa hanya sai ya hana shi ga matafiyi. (2) Da mutumin da ya yi wa wani shugaba mubaya’a babu abin da ya sa ya yi masa mubaya’a face saboda wani abin duniya, idan ya ba shi ya cika masa (mubaya’a) ya yarda, idan bai ba shi komai ba, sai ya yi fushi. (3) Da mutumin da ya tsayar da kayan kasuwancinsa bayan La’asar sai ya rika cewa: Ina rantsuwa da Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, lallai an sayar masa da kaza da kaza ne, sai wani mutum ya gaskata shi wajen saye. Sai (Annabi) ya karanta wannan aya cewa: “Lallai ne wadannan da suke sayen alkawarin Allah da rantsuwoyinsu bisa ’yan tamani kadan…” (k:3:77).
Babi na Bakwai:
Babbar mashigin ruwa (dam) gabar kogi:
88. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, dan Shihab ya ba ni labari daga Urwata daga Abdullahi dan Zubair (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai shi ya ba shi labari cewa, lallai wani mutum daga mutanen Madina ya yi husuma da Zubair a wurin Annabi (SAW) bisa wata magudanar ruwa na Harra wanda suke ban ruwan dabinai da ita. Sai mutumin Madina ya ce, “Zubair ya ki barin ruwa ya gangaro gare shi, sai suka yi husuma (suka kai kara). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka yi ban ruwanka ya Zubair sa’an nan ka bar (sake) ruwan zuwa ga makwabcinka, sai mutumin Madina ya yi fushi ya ce, “Saboda ya kasance dan Baffanka ne? Sai launin fuskar Manzon Allah (SAW) ya canza, sa’an nan ya ce; “Ka yi ban ruwa ya Zubair sa’an nan ka tsare ruwan har ya gangara zuwa ganuwa (da kamar kafa daya).” Sai Zubair ya ce, “Wallahi ina rsantuswa da Allah ina tsammani saboda ni wannan aya ta sauka cewa: “A’a, ba za su yi imani ba, face sai sun sanya ka mai hukunci ga abin da ya faru a tsakaninsu (k:4:65).” Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, “Babu wanda ya ambata daga Urwata daga Abdullahi face Laisu kadai.
Babi na Takwas:
Shayar da madaukakiya (bisa) kafin kasa:
89. An karbo daga Abdan ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Urwata ya ce, “Zubair ya yi husuma da wani mutum daga mutanen Madina, sai Annabi (SAW) ya ce, “Ka yi ban ruwan sa’an nan ka sake masa ruwa.” Sai mutumin Madina ya ce, “Saboda lallai dan Baffanka ne? Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ka yi ban ruwa ya Zubair har ruwan ya kai katanga sa’an nan ka rike. Sai Zubair ya ce, “Ina tsammani wannan aya ta sauka ne saboda haka cewa: “A’a, ba za su yi imani ba face sai sun sanya ka mai hukunci cikin abin da ya faru a tsakaninsu…” (k:4:65).