Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi Babi na Hamsin:
Abin da aka ambata game da kasuwanni. Abdurrahman dan Aufu ya ce, “Lokacin da muka isa Madina, sai na ce, “Shin akwai wata kasuwa wadda ake kasuwanci a cikinta? Sai aka ce, “Akwai kasuwar kainuka’u.” Abdurrahman ya ce, “Ku nuna mini hanyar kasuwar? Umar ya ce, “Tafiya kasuwanni ya tsare ni ga abubuwan alheri masu […]
Abin da aka ambata game da kasuwanni. Abdurrahman dan Aufu ya ce, “Lokacin da muka isa Madina, sai na ce, “Shin akwai wata kasuwa wadda ake kasuwanci a cikinta? Sai aka ce, “Akwai kasuwar kainuka’u.” Abdurrahman ya ce, “Ku nuna mini hanyar kasuwar? Umar ya ce, “Tafiya kasuwanni ya tsare ni ga abubuwan alheri masu yawa.”
568. An karbo daga Muhammad dan Sabbah ya ce: “Isma’il dan Zakariyya ya ba mu labari, daga Muhammad dan Sukat daga Nafi’u dan Jubair dan Mud’im ya ce: “A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Mayaka za su yaki Ka’aba, idan sun kasance a kasar Baida’u sai a kisfe kasa da su, farkonsu da karshensu.” Sai ta ce, “Na ce, “Ya manzon Allah! Yaya za a kisfe na farkonsu da na karshensu kasuwanninsu na cikinsu da wanda ba ya nan tare da su? Ya ce “Za a kisfe su na farkonsu da na karshensu sa’an nan a tashe su bisa niyyarsu.”
569. An karbo daga kutaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga A’mashi daga Abu Salih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Sallar mutum daya a cikin jama’a takan karu bisa ga sallarsa shi kadai a kasuwa ko gidansa da daraja ashirin da wani abu. Wannan zai kasance ne idan ya yi alwala ya kyautata alwalar, sa’an nan ya tafi Masallaci ba ya nufin komai face Sallah kuma babu abin da ya fitar da shi face Sallah, to ba zai taka wani zambiya (takon kafa) ba face an daukaka darajarsa da ita, kuma a shafe masa laifinsa da ita. Mala’iku suna salati ga dayanku matukar yana wurin sallarsa inda yake sallarsa ciki. Suna cewa: “Ya Allah! Ka jikansa, matukar bai yi hadasi ba, kuma bai cutar da kowa ba a cikinsa.” Kuma ya ce, “dayanku zai kasance na cikin ladar Sallah matukar Sallah ce ta tsare shi.”
570. An karbo daga Adamu dan Abu Iyas ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Humaid dawili daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Annabi (SAW) wata rana ya kasance a cikin kasuwa sai wani mutum ya ce: “Ya Abu kasim! Sai Annabi (SAW) ya waiga (waiwaya) gare shi sai (mutumin) ya ce, “Ba da kai nake ba, na kira wannan ne.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ku sanya suna da irin sunana, amma kada ku yi alkunya da irin alkunyata.”
571. An karbo daga Malik dan Isma’il ya ce: “Zuhair ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Wani mutum a Baki’u ya kira wani mutum da cewa, Ya Abu kasim, sai Annabi (SAW) ya waiwaya, sai mutumin ya ce, “Ba kai nake nufi ba.” Sai (Annabi) ya ce: “Ku sanya suna da irin sunana (Muhammadu), amma kada ku yi alkunya da irin alkunyata.”
572. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Ubaidullahi dan Abu Yazid daga Nafi’u dan Jubair dan Mud’im daga Abu Huraira Daushiyu (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Wata rana Annabi (SAW) ya fito a cikin wasu jama’a ba shi magana da ni, kuma ni ban magana da shi har sai ya isa kasuwar kainuka’u sai ya sauka a farfajiya (kofar ) gidan Fadima sai ya tambaya game da jikansa Alhassan cewa: “Ina yake (Alhassan)? Sai Fadima ta tsare shi bai fito da wuri ba saboda wani abu, ina tsammani lallai ita, tana sanya masa tufafi ne ko tana yin masa wanka. Sai ya fito daga baya da sauri har ya rungume shi ya sumbace shi, ya ce: “Ya Allah! Ka so shi, kuma Ka so wanda yake son shi.” Sufiyan ya ce, “Ubaidullahi ya ce, lallai shi ya ba ni labari cewa, Nafi’u ya ga dan Jubair ya yi wutiri da raka’a daya.”