Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi(1)
Babi na Uku: Hukuncin aje kare don tsaron shuka (gona): 56. An karbo daga Mu’azu dan Faddalatu ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga Yahya dan Abu Kasir daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya rike wani kare, to, ya sani lallai […]
Babi na Uku: Hukuncin aje kare don tsaron shuka (gona):
56. An karbo daga Mu’azu dan Faddalatu ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga Yahya dan Abu Kasir daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya rike wani kare, to, ya sani lallai kullum (kowane wuni) yana rage (tauye) ladar ayyukansa ne da kamar kiradi daya, face wanda ya rike kare domin tsaron gona ko kiwon dabbobi.” dan Sirin da Abu Salih sun ce, daga Abu Huraira daga Annabi (SAW) cewa: “Face (ban da) karen kiwon tumaki ko na tsaron shuka (gona) ko na farauta.” Abu Hazim ya ce, daga Abu Huraira daga Annabi (SAW) ya ce, “Karen kiwon dabbobi ko farauta.”
57. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Yazid dan Hafsat cewa, “Lallai Sa’ibi dan Yazid ya ba shi labari cewa, lallai shi ya ji Sufiyan dan Abu Zuhair cewa: Ya ji wani mutum daga kabilar Azdi na Shinu’at ya kasance daga sahabban Annabi (SAW) ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda duk ya kiwata kare ba domin ya tsare masa gona ko wata dabba ba, to, lallai ya sani yana rage (tauye) ladar aikinsa a kowane wuni da kamar kiradi. Na ce, “Shin kai ka ji shi daga Manzon Allah (S.A.W)? Ya ce, “Eh, ina rantsuwa da Ubangijin wannan daki (Ka’aba).”
Babi na Hudu: Amfani da takarkari (saniya) wajen hudar noma:
58. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Sa’ad dan Ibrahim dan Abdurrahman dan Aufu Azzuhuri ya ce: “Na ji Abu Salmata ya ce daga Abu Hurira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce; “Wata rana wani mutum yana haye bisa wata saniya sai (saniyar) ta waiwaya gare shi ta ce: “Ba a halicce ni domin wannan ba, an halicce ni domin noma.” (Mutane suka ce tsarki ya tabbata ga Allah takarkari ya yi magana! Sai (Annabi) ya ce, “Na yi imani ni da Abubakar da Umar game da haka.” Kuma (Annabi) ya ce: “Wata rana wani kerkeci ya kama daya daga cikin tumakin wani makiyayi sai makiyayin ya bi shi, sai kerkecin ya ce: Wa ke tsaronta a ranar da babu kowa cikin dajin da zai zama mai tsaro face ni.” (Annabi) ya ce, “Na yi imani ni da Abubakar da Umar game da haka.” Abu Salmata ya ce, “A wannan lokaci babu Abubakar da Umar halarce.”
Babi na Biyar: Babu laifi mutum ya ce ga wani, “Lura mini da tushen dabinon nan idan ya yi ’ya’ya mu raba tare”:
59. An karbo daga Alhakam dan Nafi’u ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari ya ce, Abu Zinad ya ba mu labari daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mutanen Madina sun ce da Annabi (SAW) ka raba mana dabinan nan a tsakaninmu da ’yan uwanmu (wadanda suka yi hijira) ya ce: “A’a, sai suka ce, “To ku lura mana da dabinan sai mu raba ’ya’yan tare.” Sai suka ce, “Mun ji mun yarda (da’a).”
Babi na Shida: Hukuncin sare itaccen dabino da wasu itatuwa:
60. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyata ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) cewa: “Lallai shi ya kona dabinan kabilar Bani Nadir kuma ya sare su. Ita ce, wadda take Buwaira saboda haka Hassan yake cewa: “Shugabannin Bani Nadir Lu’ui, sun iske kunar dabinansu da sauki a Buwaira.” (Dalilin konewa da sara saboda a samun hanyar shiga fagen yaki ne.)
Babi na Bakwai: Kamar yadda ya gabata:
61. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Sa’id ya ba mu labari daga Hanzalatu dan kaisu mutumin Madina, ya ji Rafi’u dan Khadij ya ce: “Mun kasance daga cikin wadanda suka fi mutanen Madina yawan noman dabino. Mun kasance muna hayar kasa ta hanyar ayyana abin da za mu biya mai gona bayan dibar amfanin gona. Wani lokacin amfanin yakan samu lalacewa ta hanyar burtuntuna, amma alkawarin na nan tabbatacce a tsakaninmu. Sai Annabi (SAW) ya hana mu game da haka. Amma lokacin ba mu amfani da zinari da azurfa wajen biyan kudin haya.”