Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi4
432. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Muhammad dan Ja’afar ya ba ni labari daga Humaid cewa: “Lallai shi ya ji Anas (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cin abinci a cikin wata har mu yi zaton ba zai yi azumi ba a cikinsa. Kuma yana […]
432. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Muhammad dan Ja’afar ya ba ni labari daga Humaid cewa: “Lallai shi ya ji Anas (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cin abinci a cikin wata har mu yi zaton ba zai yi azumi ba a cikinsa. Kuma yana azumi a cikin wani watan har mukan yi zaton ba zai ci komai ba a cikinsa. Kuma ba zai so ganinsa yana Sallar dare ba, face ka gan shi, ko idan yana barci face ka gan shi.” Sulaiman ya ce, daga Humaid cewa: “Lallai shi ya tambayi Anas a cikin hukuncin Azumi.”
433. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abu Khalid Ahmar ya ba mu labari, ya ce, Humaid ya ba mu labari ya ce, “Na tambayi Anas (Allah Ya yarda da shi) game da azumin Annabi (SAW) sai ya ce: “Ban kasance ba ina son ganin azuminsa cikin wata face na gan shi, ko idan yana mai cin abinci face na gan shi. Haka kuma idan ya tsayu ga sallar dare face na gan shi, ko kuma idan yana barci face na gan shi. Kuma ban taba shafar wani siliki ko karanmiski ba wanda ya fi tafin hannun Manzon Allah (SAW) taushi ba. Kuma ban taba sansanan wani turaren miski ko wani turare da ya fi kanshin Manzon Allah (SAW) ba.”
Babi na Hamshin da Hudu: Hakkin bako a cikin azumin nafila:
434. An karbo daga Is’hak ya ce: “Harun dan Isma’il ya ba mu labari, ya ce Aliyu ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba mu labari, ya ce, Abu Salma ya ba ni labari, ya ce, Abdullahi dan Amru dan Asi (Allah Ya yarda da su), ya ba ni labari ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya shiga gare ni, sai ya ambaci hadisin cewa: “(Annabi ya ce,) Bakonka na da hakkinka, kuma matarka na da hakkinta a kanka. Da karshe na ce, “Yaya azumin Dauda (AS) yake? Ya ce, “Rabin zamani (yau azumi, gobe ya sha ruwa).”
Babi na Hamsin da Biyar: Hakkin jiki a cikin azumin nafila:
435. An karbo daga dan Mukatil ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Auza’iyyu ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Kasir ya ba ni labari ya ce, dan Abu Salma dan Abdurrahaman ya ba ni labari ya ce: “Abdullahi dan Amru dan Asi (Allah Ya yarda da su), ya ba ni labari ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya fada mini cewa: “Ya Abdallah! Shin an ba ni labarin cewa, lallai kai kana azumin yini kuma kana tsayuwar dare? Na ce, “Gaskiya ne ya Manzon Allah! Ya ce, “Kada ka aikata haka, ka yi azumi ka ci abinci, ka yi nafilar dare ka yi barci, domin jikinka na da hakki gare ka, kuma idonka na da hakki a kanka, matarka na da hakki a kanka. Shin ba zai ishe maka ba, ka rika azumin kwana uku a cikin kowane wata, domin hakika kana da ladar goma ga kowace daya, haka ya zamo maka azumin lokaci dukkansa. (Abdullahi) ya ce, “Na tsananta wa kaina aka tsananta gare ni,” Na ce, “Ya Manzon Allah! Lallai ni, ina da karfin aikata haka,” sai (Annabi) ya ce, “Ka yi azumi irin azumin Dauda (AS), kada ka kara a kansa. Na ce, “Yaya azumin Dauda (AS) yake? Ya ce, “Rabin lokaci (yau azumi, gobe ya sha ruwa).” Abdullahi ya kasance yana cewa bayan da ya tsufa: “Kaitona! Da na karbi rangwamen Annabi (SAW).”