Fasto mai safarar ’yan mata ya shiga hannu a Minna
An gurfanar da wani tsohon malamin Jam’’ar Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Minna kuma limamin Kirista Fasto Adebeyo Eyitayo mai shekara 56 a gaban kotu bisa zarginsa da da safarar mutane.Fasto Adebayo Ayitayo da ke zaune a garin Maikunkele a karamar Hukumar Bosso ana zarginsa da yaudarar iyayen wasu ’yan mata 36 da […]
An gurfanar da wani tsohon malamin Jam’’ar Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Minna kuma limamin Kirista Fasto Adebeyo Eyitayo mai shekara 56 a gaban kotu bisa zarginsa da da safarar mutane.
Fasto Adebayo Ayitayo da ke zaune a garin Maikunkele a karamar Hukumar Bosso ana zarginsa da yaudarar iyayen wasu ’yan mata 36 da ya yi safarar akasarinsu zuwa birnin Fatakwal domin aikatau, kuma ana zarginsa da yin lalata da wasu daga cikinsu, ya gurfana ne a gaban Kotun Majistare ta Biyu da ke Minna.
Wata takardar koke da wata ma’aikaciya a Ma’aikatar Al’amuran Mata mai suna Malama Fatima Abubakar da ta rubuta wa ’yan sanda kan zargin mutumin da zuwa kauyuka yana jan hankalin iyayen yara su amince ya sa su a makaranta su samu ilimin zamani bayan ya yi ikirarin shi malamin addinin Kirista ne, ta sa aka kama shi.
Ana zarginsa da yin lalata da daya daga cikin ’yan matan wadda ta haifa masa da mai suna Elijah Adebayo.
Mai gabatar da kara Hassan Zakari ya bayyana wa alkalin kotun cewa wanda ake zargin yana tare da wasu daga cikin ’yan matan bayan da ya rarraba su.
Alkalin kotun Alhaji Ahmad Bima bayan nazarin lamarin, ya bayar da umarnin ’yan sanda su ci gaba da tsare wanda ake zargi a ofishinsu, domin gudanar da cikakken bincike game da lamarin, inda ya umarci Adebayo ya kawo sauran ’yan matan gaban kotun ranar 9 ga watan gobe.