Fasto Tunde Bakari ya yi hasashen yiwuwar barkewar rikici

Babban shugaban cocin ‘The Latter Rain Assembly’ Fasto Tunde Bakare, wanda kuma shi ne mataimakin dan takarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2011, ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar barkewar rikice-rikice a Najeriya a bana, musamman ma bayan an kammala manyan zabubbukan da za a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa.Da yake jawabi […]

Fasto Tunde Bakari ya yi hasashen yiwuwar barkewar rikici

Fasto Tunde BakareBabban shugaban cocin ‘The Latter Rain Assembly’ Fasto Tunde Bakare, wanda kuma shi ne mataimakin dan takarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2011, ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar barkewar rikice-rikice a Najeriya a bana, musamman ma bayan an kammala manyan zabubbukan da za a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa.
Da yake jawabi a gaban dinbin mabiyansa a cocin nasa da ke Legas, Tunde ya nuna cewa a matsayinsa na mai wa’azi, ya hango yiwuwar hargitsewar Najeriya, don haka ya zabi ya ankarar da al’umma domin gano hanyoyin da za a bi domin ganin cewa an kauce wa faruwar irin wadannan rikice-rikice, domin samun zaman lafiya da dorewar dimokuradiyya.
A jawabin nasa mai tsawo, wanda yake cike da misalai da tarihin abubuwan da suka faru da wasu al’umma na duniya a shekarun baya, ya bayyana cewa: “Dalilin da ya sa na ankarar da al’umma kan wannan batu, na yi haka ne da nufin kalubalantar shugabannin siyasa da masu rike da al’amuran tsaro, domin su dauki matakan da suka dace domin ganin an kauce wa tashe-tashen hankali kafin ko bayan zabubbukan da ake shirin gudanarwa a bana.”
Fasto Bakare ya bayyana matsaloli bakwai da a ganinsa su ne za su taimaka wajen samun matsaloli da rikice-rikice a Najeriya, musamman idan ba a dauki matakan gyara su ba. Matsalolin sun hada da cewa hukumomin zabe ba su shirya wa gudanar da zabe ba, saboda korafe-korafe da dama da suka biyo bayan samar wa masu zabe katin rijista da sauransu.
Haka kuma, ya nuna cewa rashin ingantaccen tsaro a kasa, musamman yadda kungiyar Boko Haram ke cin karenta ba babbaka a jihohin Arewa maso gabas, shi ma wata alama ce da ke nuna lalacewar harkokin tsaro, wanda hakan zai iya taimakawa a samu rikici mai yawa, kafin da kuma bayan zaben na bana.
Haka kuma ya lissafa karyewar tattalin arzikin kasa da sace-sacen dukiyar gwamnati da suka yi katutu a Najeriya kuma suka haddasa talauci ga talakawa, suna daga cikin abubuwan da za su iya jaza barkewar rikici a kasa.
Tunde ya kara da cewa, irin yadda aka cusa gaba da rashin yarda a tsakanin al’umma ta bangaren addini a tsakanin al’ummar Najeriya da wutar kabilanci da bangaranci, al’amura ne da za su iya yin tasiri wajen bayyanar rikice-rikice a kasar nana, musamman ma bayan zabubbukan da ke tafe a watan Fabrairun bana.
Sai dai kuma duk da haka, faston ya ce za a iya kauce wa irin wadannan rikice-rikice, musamman idan aka dauki matakan da suka dace. A wannan dalili ne ma ya bayyana wadansu shawarwari, wadanda ya ce idan aka dauke su, Najeriya za ta dawwama, a samar da zaman lafya da kuma tsarin dimokuradiyya mai dorewa.
A shawararsa ta farko, Tunde ya ce ya kamata a dakatar da gudanar da zaben da ake shirin yi a bana, a madadinsa, a kafa gwamnatin riko, inda shi Shugaba Jonathan zai jagoranta, daga bisani idan an samu yanayin da ya dace, sai a gudanar da sahihin zabe, wanda zai samar da gwamnati mai karfi a dimokuradiyyance.
Haka kuma ya bukaci a kaddamar da kudurorin da aka zartar a babban taron kasa da aka gudanar a bara. Sannan ya nemi a shirya sabon kundin tsarin mulki, wanda zai zama mai adalci da kula da bukatu da muradun al’umma.
“Muddin aka dauki irin wadannan matakai, babu shakka Najeriya za ta kauce wa rikice-rikice, dimokuradiyya mai karfi za ta tabbata sannan kuma a samu zaman lafiya a kasa.” Inji Tunde Bakare.