Fasto ya harbe ƙaramin yaro har lahira da a coci
Wani fasto ya shiga hannu bayan da ya ɗirka wa wani ƙaramin yaro harbi har lahira a Jihar Imo.
Wani fasto ya shiga hannu bayan da ya ɗirka wa wani ƙaramin yaro harbi har lahira a Jihar Imo.
’Yan sanda sun kama Fasto Moses Enyiaka ne bisa zargin harbe yaron har lahira saboda ya harba abubuwa masu qara a cikin harabar coci.
Wannan ɗanyen aiki ya faru ne a lokacin da ake tsaka da ibadar tarbar Sabuwar Shekarar 2025 a Cocin St Columbus Parish da ke yankin Amamio na Ƙaramar Hukumar Ikeredu ta jihar.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ASP Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa sun fara bincike domin gano ainihin musabbabin abin da ya faru.
- NAJERIYA A YAU: “Makomar Ɓangaren Ilimi A 2025 Tana Cikin Haɗari”
- An raunata wasu a rikicin matasa da ’yan banga a Neja
Jami’in ya ce ba su san yadda limamin cocin ya samu bindigar da ya yi amfani da ita ba, amma suna ci gaba da bincike.
Aminiya ta gano cewa rundunar ’yan sanda ta haramta kunna abubuwan masu ƙara a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a Jihar Imo.
Ko a ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 2024, sai da Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Imo, Aboki Ɗanjuma, ya sake nanata cewa dokar haramcin tana nan ba ta daina aiki ba.