Fasto ya je wa’azi coci da bindigar AK-47 a Abuja
Sai dai babu tabbacin ko bindigar na dauke da harsashi ko a’a
Wani Fasto mai suna Uche Aigbe da ya hau dandamalin coci da bindiga kirar AK-47 don yin wa’azi ranar Lahadi a Abuja ya jefa mabiyansa cikin rudani.
Faston dai ya dauko bindigar ne lokacin da yake takawa zuwa dandamalin da zai yi wa’azin, nan da nan kuma mabiyansa suka rude saboda rashin sanin abin da zai biyo baya.
- DSS ta gayyaci Fani-Kayode saboda kalamansa kan yunkurin juyin mulki
- Babu wanda ya jefi Buni a yakin neman zabe —APC
Ganin hakan ne kuma ya sanya cikin barkwanci ya fara cewa ya zo ne da shirinsa saboda wasu mutane da ke neman shigar masa hanci da kudundune.
Ya kuma ce daukar bindiga a wannan lokacin ya zama wajibi, la’akari da yadda ake samun bara-gurbin Fasto-Fasto din da ke daidaita rayuwar mutane.
Sai dai babu wani rahoto da ya tabbatar da bindigar na dauke da harsashi ko a’a.