Fasto ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a kango

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama wani Limamin Kirista cocin Gathering Ebangelical Church of God da ke Papalanto a karamar Hukumar Ewekoro da ke jihar mai suna Fasto Oluwatobiloba Ipense bisa zarginsa da kashe budurwarsa mai suna Raliat Sanni don yin tsafi da sassan jikinta. Rahotonni sun ce,  Faston ya gutsere kan matar da […]

Fasto ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a kango

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama wani Limamin Kirista cocin Gathering Ebangelical Church of God da ke Papalanto a karamar Hukumar Ewekoro da ke jihar mai suna Fasto Oluwatobiloba Ipense bisa zarginsa da kashe budurwarsa mai suna Raliat Sanni don yin tsafi da sassan jikinta.

Rahotonni sun ce,  Faston ya gutsere kan matar da hannuwanta biyu da kuma wasu sassan jikinta don yin tsafi sannan ya binne gawar a wani kango da ake kyautata zaton wani coci ne da ba a karasa gininsa ba.

Marigayiya Rafiat, tana gudanar da sana’ar gyaran gashi ne kuma bazawara ce mai ’ya’ya biyar.

A ranar Talatar da ta wuce ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun Ahmed Iliyasu ya jagoranci tawagar ’yan jarida da al’ummar yankin zuwa kangon da faston ya binne marigayiyar.

Kwamishinan ya ce sun samu rahoto ne daga wajen ’yan uwan marigayiya Rafita a ranar 21 ga Maris, 2018 game da bacewar marigayiyar inda suka shiga binciken sirri daga nan ne suka gano Faston yana hulda da matar.  Bayan an tuhume shi ne sai ya tabbatar da cewa shi tare da hadin gwiwar wani abokinsa da shi ma Fasto ne a wani coci mai suna Daniel Sopeju ya taimaka masa wajen gudanar da wannan aika-aika. Daga nan rundunar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen kamo Daniel don su fuskanci hukunci.

Kwamishina Iliyasu ya ce da zarar rundunarsa ta kammala bincike za ta tasa keyar wadanda ake zargin zuwa kotu don su fuskanci hukunci.

Daga nan ya yi kira ga jama’a su rika yin taka tsan-tsan da irin mutanen da suke yin hulda da su.