Fasto ya rasu bayan ya ce a binne shi da rai
Ana tuhumar mutum biyar ’yan gida daya da kisan wani limanin Kirista bayan an binne shi da rai kamar yadda ya umarta. Faston mai suna, Shamiso Kanyama, ya rasa ransa ne bayan da aka kira shi aikin korar aljanu daga wani gida a wani kauye da ke kasar Zimbabwe, kamar yadda jaridar Zed 24 News […]
Ana tuhumar mutum biyar ’yan gida daya da kisan wani limanin Kirista bayan an binne shi da rai kamar yadda ya umarta.
Faston mai suna, Shamiso Kanyama, ya rasa ransa ne bayan da aka kira shi aikin korar aljanu daga wani gida a wani kauye da ke kasar Zimbabwe, kamar yadda jaridar Zed 24 News ta ruwaito.
Wadanda ake zargin su ne: Leanmore Mutero da Tonderai Muswere da Michael Muchengeti da Manasa Mutero da kuma Nicholas Mutero. Kuma dukkansu sun bayyana a gaban Babban Kotun birnin Harare a zaman kotun na makon jiya.
An ruwaito cewa marigayin ne ya bukaci jama’a da su binne shi da rai saboda a cewarsa ya samu karin karfin fatattakar miyagun aljanu wadanda suke kawo kashe-kashe a gidan da suka gayyato shi. Daga nan ne sai aka haka wani kabari aka binne shi, amma bayan da mutanen suka kwashe lokaci mai tsawo ba tare da jin duriyarsa ba, sai suka tone ramin, inda suka same shi a mace.
Wani wanda ya ga al’amarin, Joseph Taderera, ya bayyana wa kotun cewa: “Faston ne da kansa ya taimaka wajen haka kabarin tun da farko kafin daga bisani ya yi addu’a ya fada ciki, ya kuma kwanta rub da ciki gabanin ya ce a rufe shi da kasa.”
Joseph ya kara da cewa akwai lokacin da ya ce adakata da zuba kasar, amma sai faston da kansa ya kara ba da umarnin ci gaba da binne shi, tare da ba da tabbacin cewa kada su damu zai taso daga kabarin lafiya lau. Kuma marigayin ya ce: “A ce Joseph ya yi masa shuru domin yana damun mala’ikun da yake gana wa da su.”