Fasto ya shiga hannu kan zargin satar yara 17

An kama wani fasto mai suna Fasto Kombot dan asalin Jihar Filato da yara kanana 17 da ake zargin ya sato su ne.An kama faston ne a hayin kogin Benuwai a garin Ibbi da ke cikin karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Litinin a lokacin da yake kokarin […]

Fasto ya shiga hannu kan zargin satar yara 17
Fasto ya shiga hannu kan zargin satar yara 17

An kama wani fasto mai suna Fasto Kombot dan asalin Jihar Filato da yara kanana 17 da ake zargin ya sato su ne.
An kama faston ne a hayin kogin Benuwai a garin Ibbi da ke cikin karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Litinin a lokacin da yake kokarin tafiya da su wani yanki a Jihar Filato.
Kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilinmu wanda ake zargi da sato yaran har an yi masa fito daga garin Ibbi zuwa ketaren kogin Benuwai amma sai masu fito suka tuhume shi kan inda ya fito da yaran da kuma inda zai kai su
Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa Faston ya kasa bayar da bayani mai gamsarwa game da inda ya fito da yaran da kuma dangantakarsa da su.
Yara wadanda suka hada da maza da mata mafi yawansu ba su wuce shekara hudu zuwa bakwai ba, kuma yawancinsu ba sa iya magana wanda ya sa ake zaton ko ya ba su magani ne da ya gusar da hankalinsu.
Majiyar ta fada wa wakilinmu cewa da aka matsa wa Fasto Kombot da tambaya sai ya ce shi faston ne a wani coci da ke Jihar Filato amma kuma ya kasa fadin dangantakarsa da yaran.
Ganin wanda ake zargin ya kasa bayar da amsa mai gamsarwa kan alakarsa da yaran ne sai masu fiton da sauran jama’ar da ke bakin kogi suka sanar wa ’yan sanda inda suka kama Faston.
Shugaban karamar Hukumar Ibbi, Alhaji Iliya Mohammed ya tabbatar da kama wanda ake zargin. Alhaji Iliya Mohammed ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa har an yi wa  wanda ake tuhumar fito a kwale-kwale amma saboda yawan yaran kuma ga su masu kananan shekaru sai aka fara tuhumarsa.
Shugaban ya ce wanda ake zargin ya ce shi Fasto ne a wani coci a Jihar Filato, kuma ganin da yawa daga cikin yaran Musulmi ne shi ya sa ake zargin sato su ya yi.
Alhaji Iliya ya ce tuni aka mika wanda ake tuhumar ga ’yan sanda kuma an wuce da shi da yaran zuwa Hedkwatar Rundunar ’Yan sanda ta Jihar Taraba da ke Jalingo.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar ASP Joseph Kwaji ya tabbatar da kama wani mutum da yara 17 da ake zargin ya sato su ne.ASP Joseph Kwaji ya ce za a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin domin a gano inda wanda ake tuhumar ya dauko yaran da kuma inda zai kai su.