Fasto ya ’yanto fursunoni Musulmi domin azumi

Fasto Yohanna Buru wani limamin Kirista ne da ke zaune a jihar Kaduna wanda a ranar Juma’ar da ta gabata ya ’yanto wadansu fursunoni Musulmi su shida albarkacin watan azumin Ramadan, Fursunonin suna tsare ne a Babban Gidan Yarin Kaduna saboda ko dai sun kasa biyan kudin tarar da aka yi masu, ko kuma laifukan […]

Fasto ya ’yanto fursunoni Musulmi domin azumi
Fasto ya ’yanto fursunoni Musulmi domin azumi

Fasto Yohanna Buru wani limamin Kirista ne da ke zaune a jihar Kaduna wanda a ranar Juma’ar da ta gabata ya ’yanto wadansu fursunoni Musulmi su shida albarkacin watan azumin Ramadan, Fursunonin suna tsare ne a Babban Gidan Yarin Kaduna saboda ko dai sun kasa biyan kudin tarar da aka yi masu, ko kuma laifukan da suka sa ake tsare da su ba su taka kara sun karya ba. A zantawarsa da wakilinmu, ya yi karin haske game da sakin fursunonin da aikace-aikacen da yake gudanarwa don wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna da kuma sasantawa tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka gabatar da kanka?
Fasto Buru: Sunana Fasto Yohanna Y D Buru, Shugaban kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya da Sasantawa ta (Peace Rebibal and Reconciliation Foundation), bugu da kari ni ne limamin Cocin Christ Ebangelical and Intercessory Fellowship Ministry da ke unguwar Sabon Tasha, Kaduna. An haifi ni a garin Kwoi da ke yankin karamar Hukumar Jaba ta jihar Kaduna a shekarar 1966. Na yi makarantar firamare a LEA Kwoi, bayan da na kammala ne na wuce wata makarantar sakandare da ke garin Kagoro a shekarar 1982. Daga nan ne na ci gaba zuwa Makarantar Horor Limaman Kirista, wato ECWA Seminary da ke unguwar Farar Gada a jihar Filato, inda na samu shaidar difloma a shekarar 1999, a shekarar 2004 kuma na samu takardar shaidar digiri.
Aminiya:Wane dalili ne ya ja hankalinka ka yi tunanin taimaka wa wadanan fursunonin Musulmi?
Fasto Buru: Akwai abubuwa kusan guda uku da suka ja hankalina har na yi wannan aikin. Na farko ya samo asali ne daga aniyata ta wanzar da zaman lafiya da fahimta tsakanin mabiya addinai daban-daban a kasar nan, musamman ma Musulmi da Kirista. Saboda idan ka ji rikicin addini a Najeriya, rikici ne wanda ya shafi wadannan addinan biyu. Ba za ka taba ji hakan ya faru tsakanin daya daga cikin addinan nan da kuma mabiya addinin Gargajiya ba. Dalili da wannan a farkon shekarar nan na ga ya dace na kafa wannan kungiyar don sasantawa da kuma wanzar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista. Dalili na biyu shi ne, na yi imani da addu’a. Na yi amanna da cewa kowane mutum zai iya yin addu’a kuma Allah Ubangiji ya karba ba tare da la’akari da shi Musulmi ne ko Kirista ne ba, saboda Allah ne Mahaliccin kowa da kowa. Wadansu daga cikin mutanen nan kuma ba wani laifi ne suka yi da ya taka kara ya karya ba. Wannan ya sa bisa la’akari da ganin girman watan azumin Ramadan wanda lokaci ne da Allah ke karbar addu’a kamar yankan reza, kuma mutanen da ke tsare a kurkuku mutane ne kamar kowa, kuma kila idan suka yi nadama Allah Ya karbi addu’arsu. Abu na uku shi ne yadda kasar nan ba ta zaune lafiya, ba mu sani ba ko mutanen nan da suka fito daga gidan yari, idan suka yi addu’a Allah Ya amsa Ya zaunar da mu lafiya. Wadannan suka sa na ga ya dace a ce na nuna wa Musulmi kauna irin wadda Yesu Almasihu ya koyar a cikin littafi mai tsarki, wato Baibul.
A fahimta ta ’yanto fursunonin zai fi tasiri ga al’umma maimakon dimbin kasidu da ake yawan gabatarwa kan mahimmancin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Kirista da Musulmi.
Aminiya: Wacce hanya ka bi wajen zaben fursunonin shida cikin dimbin fursunonin da ke tsare a kurkukun?
Fasto Buru: Yana da kyau jama’a su fahimci cewa ba wannan ba ne karon farkon da muka fara ’yanto fursunoni a lokacin watan azumin Ramadan ba, a bara ma mun yi wannan aikin alherin inda muka taimaka wajen sallamar fursunoni Musulmai guda takwas. A wancan karon ni ne da kaina na zabo su. Amma a bana an ce sam, sai dai na bi ta hannun Shugaban Hukumar da ke Kula da Gidajen Yarin da ke jihar Kaduna domin gabatar da niyyata a rubuce. Na yi hakan ba tare da wani bata lokaci ba. Kodayake a takardar na bukaci su saki fursunoni 30 ne, amma da yake su ne da kansu suka yi aikin tantancewar da zabo fursunonin, bayan sun kammala aikinsu ne suka shaida min cewa za su iya sallamar mutum shida ne kawai. Na biya kudi aka sake su nan take. Har ila yau, a yanzu haka na fara shirin kara jagorantar sakin wadansu fursunonin kafin karshen watan Ramadan saboda fatana shi ne akalla a ce su ma wadannan su yi bukukuwan karamar Salla a gidajensu tare da iyalansu kamar kowa.
Aminiya: Wane tanadi aka wa wadannan fursunonin shida bayan sakinsu don gudun kar su koma gidan jiya?
Fasto Buru: Da farko mun ba dukkanninsu kudin motar da zai kai su gida. A yanzu kuma mun fara tattaunawa da su domin ganin yadda za mu taimaka musu da jari don fara sana’o’i. Muna kuma da wani shiri don ba da horo kan  sana’o’in hannu ga masu sha’awa daga cikinsu. Shakka babu wannan zai taimaka wajen magance komawa gidan jiyan da ka ce.
Aminiya: Me ya sa Musulmi ne kawai ka ke ’yantowa daga gidan wakafi?
Fasto Buru: Domin ina so na tabbatar masu da aniyyata ta kaunar zaman lafiya da su.
Aminiya: Wane martani kake samu daga bangaren ’yan uwanka mabiya addinin Kirista dangane da wannan aikin?
Fasto Buru: A gaskiya wadansu suna sukana sosai, suna cewa wai ni na Musulunta ne. Wadansu kuma cewa suke wai kudi ake biyana don gudanar da wadannan ayyukan, ko farfaganda nake, ko kuma ina yi ne domin neman wani mukamin siyasa a nan gaba. Amma duka wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne. Ina yi ne domin Allah. Akwai wani lokaci da wadansu suka tunkare ni da bukatar ko zan shiga siyasa, amma na ce ba na bukata, su kai kasuwa. Na gode wa Ubangiji da Ya ba ni matsayin fasto, Alhamdulillah.
Wadansu sun jahilci abun ne, amma ni Kirista ne. Kuma suka ba za ta hana ni ci gaba da wadannan ayyukan alherin ba. Ya kamata mutane su gane cewa kowanenmu na bukatar zaman lafiya. Zan so a fahimci cewa kalubalen ba wai kawai daga bangaren Kiristoci ba ne kawai, a’a ina samun suka har daga wadansu Musulmi inda wadansu ke cewa wahalar banza nake yi.
Aminiya: Ko hakan na sanya gwiwarka yin sanyi?
Fasto Buru: Ko daya, saboda Allah ne kawai ya san abubuwan da ke zuciyar kowa. Ya san niyyata da imanina, don haka suka ko zargi ba za su sa na fasa wadannan ayyukan ba.
Aminiya: Za mu so mu ji yadda  tasowarka ta kasance?  
Fasto Buru: Na taso ne dai a unguwar Badarawa da ke yankin karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, kusan shekara 30 da suka wuce, wadda unguwar galibin mazaunanta Musulmi ne. Kuma a wancan lokacin ana zaune lafiya ne, sabanin yanzu da ake zaman doya da manja. Abu na biyu shi ne na kwashe shekara kusan 30 ina bincike kan addinin Musulunci da Musulmai. Wannan ya sa na fahimci addinin sosai kuma ya gina min kyakkyawar fahimta kan Musulmai. Wanda kafin na fara binciken, na zaci addinin Musulunci addini ne na ’yan tada zaune tsaye. Amma bayan da na yi nisa a bincikena, sai na gane cewa addini ne da ke matukar kaunar zaman lafiya.
Aminiya:Wane dalili ne ya sa ka fara gudanar da binciken?  
Fasto Buru: Dalilin shi ne, a shekarar 1986 na yi sha’awar shiga addinin Musulunci amma sai Allah bai nufe ni ba. A lokacin ne na fara bincike don neman sanin mene ne Musulunci. Na ci gaba da neman sani kan addinin, inda a shekarar 1990 na so shiga makaratar koyon harshen Larabci ta Kano (SAS) amma Allah bai yarda ba. A gaskiya Allah ne kawai bai nufe ni da zama Musulmi ba.
Aminiya: Ka taba samun wani taimako daga gwamnati?
Fasto Buru: A’a ban taba samun wani taimako  ko wani martani  daga gare ta ba. Babu wani taimako da na taba samu daga wata gwamnati ta gida ko ta kasashen ketare. Daga aljihuna nake gudanar da wadannan ayyukan, ban taba samun taimako daga wajen kowa ba. Wannan ya sa wani lokaci ma har sai na ci bashi don ganin na gudanar da wadansu ayyukan. Allah ne kawai ke taimakona.
Aminiya: Akwai wadansu ayyuka da kake gudanarwa bayan aikin taimakawa wajen sakin fursunoni daga kurkuku?
Fasto Buru: Suna da dama. A shekara biyu a jere na shirya Maulidi don tunawa da haihuwar Manzon Allah (SAW), an gudanar da na bara a dakin taro na Women Multipurpose Centre, na bana kuma a dakin taro na Gidan Arewa, duka a garin Kaduna. Hakazalika, shekara biyu ke nan da muke gudanar da bukukuwan Kirsimeti tare da mabiya addinin Musulunci da suka kai kusan su dubu a gidana da ke unguwar Sabon Tasha. Har ila yau, mun samu nasarar sasanta al’ummomin da ba sa ga maciji da juna a Kasuwar Magani da Tirkaniya da sauran wurare a ciki da wajen kasar nan, kamarsu Jamhuriyar Nijar da kasar Benin.
A bana kawai na halarci taron Maulidi fiye da guda 30. Ciki har da Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass wanda aka gudanar a watan Mayun da ya wuce a jihar Gombe. Na taba ziyartar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III a fadarsa da ke Sakkwato. Ko a ranar Lahadin da ta gabata na je Zariya inda na halarci karatun Tafsin din Sheikh Ibrahim Zakzaky. Bayan da aka kammala ne kuma muka wuce gidansa da ke unguwar Gyallesu inda muka yi buda-baki tare da dimbin jama’a.
Aminiya: Ya batun iyali?
Fasto Buru: Ina da mata daya da ’ya’ya biyar.