Fasto ya yi murabus domin goyon bayan auren mace fiye da daya

Fasto Ogochukwu ya yi ikirarin samun wahayi da ke umartasa da ya goyi bayan auren mace fiye da daya

Fasto ya yi murabus domin goyon bayan auren mace fiye da daya

Wani babban limamin coci ya yi murabus daga matsayinsa inda ya shiga cikin masu goyon bayan auren mace fiye da daya.

Rabaran Ogbuchukwu Makuo Lotanna da ke Ikilisiyar Cocin Anglican a Nnewi, Jihar Anambra, ya yi ikirarin samun wahayi da ke umartar sa ya shiga cikin magoya bayan auren mace fiye da daya a Najeriya.

Malaman Kirista dai sun bayyana cewa addinin ya haramta auren mace fiye da daya da kuma sakin aure.

Amma Rabaran Ogbuchukwu ya ce, “Sanin kowa ne cewa coci, musamman na Anglican, na yin wa’azi cewa a nisanci auren mace fiye da daya, amma Allah Ya ganar da ni gaskiya, cewa yin hakan ba haramun ba ne.

“Abin da Allah Ya haramta shi ne kowane irin sakin aure da kuma zina — ga mai aure ko wanda ya taba yin aure da ma wanda bai taba yi ba.”

Rabaran din, ya ci gaba da cewa wahayin da ya samu zai taimaka wajen yada auren mace fiye da daya tare da rage zinace-zinace a Najeriya.

Rabaran Ogbuchukwu Lotanna wanda dan asalin Mbanagu Otolo a Nnewi, ya ce sunan tafiyar tasu ta goyon bayan auren mace fiye da daya Gideonites, kuma za su bude wurin ibadarsu da suna Gideonites’ Temple.

A ranar 22 ga watan Disamban 2019 ne aka rantsar da Rabaran Ogbuchukwu Lotanna mai mata daya, a matsayin babban limamin cocin Anglican na Cathedral Church of St. Mary’s da ke Uruagu a garin Nnewi.

Zuwa lokacin da wakilinnmu ya kammala hada wannan rahoto, babu wata sanarwar a hukumance ba game da lamarin daga hukumomin cocin Anglican da ke kula da yankin Nnewi.

Wakilinmu ya gano cewa a halin yanzu shugabancin cocin na yankin na ci gaba da gudanar da babban taron manyan limamansa na shekarar 2022.

Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 95 a ƙasar Tibet

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m