Fasto ya yi wa mambobin cocinsa 2 fyade a Legas
Kotun ta aike da shi kurkuku a kan haka
Wata kotu da ke Ikejan Jihar Legas a ranar Litinin ta aike da wani limamin coci, Daniel Oluwafeyiropo, gidan yari, bisa zarginsa da yi wa mambobin cocin da yake jagoranta su biyu fyade.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa alkalin kotun, Mai Shari’a Ramon Oshodi ne ya yanke wa limamin cocin ta “I Reign Christian Ministry” hukuncin dauri a gidan gyaran hali na Kirikiri, har zuwa lokacin da zai cika sharudan belin nasa.
- INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaben Adamawa
- Buhari zai kaddamar da titin Kano-Kaduna a watan gobe – Fashola
Alkalin dai ya bayar da belin mutumin ne a kan kudi Naira miliyan 20 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.
Ya kuma ce doe masu tsaya masan su kasance suna da ginanniyar kadara a Jihar Legas, wacce darajarta za ta kai kimar kudin belin, da kuma shaidar biyan haraji ta shekara uku.
Daga nan ne ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar tara bga watan Mayu mai zuwa.
Tun da farko dai, lauyan wanda ake zargi, Olokunle Oyewole ne ya bukaci kotun ta bayar da belin wanda yake karewa ranar 10 ga watan Afrilu, saboda ko a baya bai taba kin bayyana ba a duk lokacin da aka bukace shi.
Tun da farko dai an gurfanar da limamin ne bisa zarginsa da laifuka biyu da ke da alaka da aikata fyade. Sai dai ya musanta aikata laifin.
Masu shigar da kara dai sun shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a watan Yunin 2020 a rukunin gidaje na Ikota da ke Lekki a Jihar ta Legas.
Sun ce laifin ya saba da tanade-tanaden sashe na 260 (2) na kundin manya laifuka na jihar na shekara ta 2015. (NAN)