Fasto ya yi wa mambobin cocinsa 20 ciki
’Yan sanda a Jihar Enugu sun kama wani fasto mai suna Timothy Ngwu, da ke shugabancin cocin bineyard Ministry of the Holy Trinity da ke Ihe-Owerre, Nsukka, bisa zargin yi wa mambobin cocinsa 20 ciki.Rahotanni sun ce kafin kama fasto a ranar Juma’ar da ta gabata, ya rika nuna wa mambobin cocin cewa yana bin […]

’Yan sanda a Jihar Enugu sun kama wani fasto mai suna Timothy Ngwu, da ke shugabancin cocin bineyard Ministry of the Holy Trinity da ke Ihe-Owerre, Nsukka, bisa zargin yi wa mambobin cocinsa 20 ciki.
Rahotanni sun ce kafin kama fasto a ranar Juma’ar da ta gabata, ya rika nuna wa mambobin cocin cewa yana bin umarnin Ubangiji ne, kuma matan da ya yi wa ciki sun hada da matan aure da ’yan mata.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Enugu, DSP Ebere Amaraizu, ya ce “Faston ya yi da’awar yana cika umarnin annabta da sakon wahayi ne wajen yin abin da ubangiji ke so, na ya yi ciki ga duk matar da ruhu mai tsarki ya zaba kuma ya nuna masa ba tare da lura tana da aure ko babu ba. Kuma idan matar ta haihu jaririn zai ci gaba da kasancewa a coci tare da mahaifiyarsa har karshen rayuwarsu.”
Mamayar da jami’an yaki da fataucin yara a karkashin DSP Gloria Udoka suka cocin bayan samun korafi daga matar faston mai suna beronica Ngwu ne, kan yadda ake lalata da mata a cocin da ke kawo yawaitar samun juna biyu a tsakanin matan aure da marasa aure ya sa aka gano haka.
An gano cewa ya fake da wannan da’awa na bin umarnin ubangiji inda ya yi wa ’yar uwar matarsa ciki.
’Yan sanda sun ce wasu daga cikin matan aure da ke zuwa cocin suna zaune tare da shi bayan da ya yi musu ciki.
Da kare kansa kan zargin faston ya ce yana da mata biyar da ’ya’ya 13 baya ga sa-daka da dama da yake da su, wadanda suka zo masa bisa umarnin ubangiji. Ya ce, ba ya yin komai da matar aure, sai an samu amincewa da yarjejeniya a tsakaninsa da mijinta, kamar yadda ruhu mai tsarki ya umarce shi.
Calista Omeje da Assumpta Odo sun ce sun bar mazansu sun koma wurin faston ne saboda bin umarnin annabta don cika burin ubangiji. Calista mai ’ya’ya 10 da mijinta, ta ce Fasto Timothy ya yi mata ciki, sai dai jaririn ya mutu daga baya. Ta ce ta aurar masa da ’yarta domin ya yi mata ciki saboda bin umarnin ubangiji. Ita kuwa Assumpta Odo ta ce tana da aure da ’ya’ya takwas, kuma faston ya yi mata ciki ita da ’yarta.