Faston da ke karbar N310,000 ‘kudin shiga Aljannah’ ya gurfana a gaban kotu

Ana zargin Fasting da yunkurin aikata damfara

Faston da ke karbar N310,000 ‘kudin shiga Aljannah’ ya gurfana a gaban kotu

Wasu masu ibada a coci

An gurfanar da wani Fasto a gaban Babbar Kotun Majistare da ke Ado Ekiti a Jihar Ekiti, bisa zargin bukatar ’yan cocin shi su biya N310,000 a matsayin kudin shiga Aljannah.

Ana dai tuhumar Faston mai suna Noah Abraham na cocin Christ High Commission Ministry, da laifin yin karya da niyyar aikata damfara.

Rahotanni sun ce kwanan nan Faston ya tare a garin Omuo Oke na Jihar ta Ekiti, bayan ya baro Jihar Kaduna.

Dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Johnson Okunade, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 27 ga watan Afrilun 2022.

Ya ce, “Fasto Noah Abraham ya gabatar da kansa gaban mabiya cocin yana bukatar da su biya kudi tsakanin N300,000 zuwa N310,000 kudin ceto don su samu shiga Aljannah.

“Laifin ya saba da sashe na 416 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Ekiti na shekarar 2012,” inji dan sandan.

Sai dai bayan an karanta masa kunshin tuhumar, wanda ake zargin ya ce ya fahimta, amma ya ki amincewa ya amsa laifin.

Daga nan ne lauyan wanda ake zargin, Adunni Olanipekun, ya roki kotun da ta ba da shi beli domin a shirye suke su cika dukkan sharudan da ake bukata har zuwa lokacin da za a ya ke hukunci.

Sai dai dan sanda mai shigar da kara bai soki bukatar bayar da belin ba.

Daga nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a, Titilola Olaolorun, ya ba da belin Faston kan N100,000 tare da mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda dole su kasance suna da katin zama dan kasa na Najeriya.

Alkalin ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Mayun 2022 don ci gaba da sauraron karar.