Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

An kama wasu mata biyu a ƙananan hukumomin Essien Udim da Nsit Ubium kan zargin safarar ƙananan yara.

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan Jihar Akwa Ibom ta tsare wani fasto mai suna Louis Akpojotor Mevoweoyo bisa zarginsa da laifin yi wa ‘yarsa mai shekara 14 fyaɗe.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Timfon John ce ta sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a hedkwatar rundunar da ke Uyo.

Wannan fasto ya shafe shekara biyu yana yi wa ‘yar tasa fyaɗe inda tun tana kimanin ‘yar shekara 12 da haihuwa ya fara kusantar ta kamar yadda kakakin ’yan sandan ta bayyana.

Kakakin ta ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Ta ce a ƙoƙarin da rundunar ke ci gaba da aiwatarwa wajen yaƙi da ɓata gari, ta kuma kama wasu mata biyu da laifin safarar ƙananan yara.

DSP Timfon ta ce ana zargin matan sun ɗauko yaran ne daga ƙauyukan Ikot Edibom da Mkpatak da ke ƙananan hukumomin Essien Udim da Nsit Ubium.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa