Fataken dabbobi sun koka da takurawar da ake masu a Kudu
Alhaji Muhammadu Attahiru, shugaban kungiyar fatake masu safarar dabbobi da kayan abinci ya koka da yadda ’yan masu amsar haraji ke matsa masu a yayin sana’arsu daga Arewacin kasar nan zuwa jihohin Kudu.A wata zantawa da Aminiya a lokacin ziyarar aiki na musamman da shugaban kungiyar ya kawo a garin Benin, fadar mulkin gwamnatin Jihar […]
Alhaji Muhammadu Attahiru, shugaban kungiyar fatake masu safarar dabbobi da kayan abinci ya koka da yadda ’yan masu amsar haraji ke matsa masu a yayin sana’arsu daga Arewacin kasar nan zuwa jihohin Kudu.
A wata zantawa da Aminiya a lokacin ziyarar aiki na musamman da shugaban kungiyar ya kawo a garin Benin, fadar mulkin gwamnatin Jihar Edo a makon jiya, ya bayyana dalilin zuwansa a jihar. “Zuwana nan Jihar Edo ya kunshi irin korafe-korafen da mambobinmu ke yi a kan batun tsauwala musu kudaden haraji na kan hanyoyin Kudu da wasu zauna gari banza suka gane suke yi musu. ’Yan-ba-ni-na-iya na jihohin Kudu suna cin karensu babu babbaka wajen karbar kudade masu yawa daga hannun fatakenmu da sunan haraji, wanda ba ya bisa kan ka’ida ta gwamnati. Wannan shi ne dalilin zuwana, domin in sadu da masu ruwa da tsaki da suke fada a ji na gwamnatocin wadannan jihohin. Kuma kafin in zo sai da na yi magana da Sufeta-Janar na ’yan sanda kuma ya tabbatar mani da cewa hukuma ta zauna ta tabbatar da ce wa an janye maganar karbar haraji a kan hanyoyi gaba daya.” Inji shi.
Ya fadi cewa kudaden da suke biyan ya zarce yadda ake tunani. “A takaice dai a yanzu haka daga Borno, Yobe da Adamawa, idan ka loda kaya ka nufi Fatakwal sai ka kashe kusan N180,000 wani zubi har N200,000.”
Daga nan kuma sai shugaban ya shawarci gwamnatocin jihohin Kudu da cewa su tsara abin da zai kawo hadin kai da fahimtar juna ga ’yan kasuwa ’yan asalin Arewa; ba wai su bi suna takura musu da nuna musu kabilanci ba; domin yin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.
“Kuma za mu ci gaba da ba gwamnati hadin kai da biyan haraji na gaskiya kuma koda wani fili ne gwamnatin ta kebe ta ce a nan za mu sayar da kayanmu; to lallai za mu yarda domin gwamnati ta al’ummar kasa ce, don haka za mu biyata inda za mu loda kaya da inda za mu sauke kayan kuma a ba mu rasidi. Amma ba irin yadda wasu jihohin Kudu suka dauke mu kamar mu ba ’yan Najeriya ba, su rika tatsarmu a hanyoyinsu. Don haka shawara a nan ita ce, su tsaya a kan abin da dokar kasa ta yarda da shi wajen karbar harajin.”
Y kuma yi kira ga mambobin kungiyarsu da cewa su tabbatar suna bin dokar kasa wajen biyan kudin shiga na gwamnati daga inda suke daukar kaya da inda za su sauke.