Fatanmu zaben kananan hukumin Kano ya fi na baya inganci
Idan Allah Ya so gobe Asabar ce Jam`iyyun siyasa 19, za su fafata ya junansu don neman kujeru 44, da Kansiloli 484, na shugabanni da Kansilolin kananan Hukumomin jihar Kano 44. Zaben da Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano za ta gudanar. Wasu daga cikin jam`iyyun da za su jarraba farin jininsu ga […]
Idan Allah Ya so gobe Asabar ce Jam`iyyun siyasa 19, za su fafata ya junansu don neman kujeru 44, da Kansiloli 484, na shugabanni da Kansilolin kananan Hukumomin jihar Kano 44. Zaben da Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano za ta gudanar. Wasu daga cikin jam`iyyun da za su jarraba farin jininsu ga mutanen jihar, sun hada da jam`iyyun adawa irin na ACCORD da PDM da NCP da PDP da LP da kuma jam`iyyarAPC mai mulkin jihar ta Kano.
Wannan zabe in an yi shi, shi ne irinsa na hudu da ake gudanarwa cikin Majalisun kananan Hukumomin jihar ta Kano tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, bayan zaben bai daya da sojoji suka yi a zaman mika mulki da suka hada da na Majalisun kananan Hukumomi. A lokacin gwamnatin jam`iyyar APP da ta yi mulkin shekaru takwas, bayan ta karbi mulki daga hannun PDP a shekarar 2003, ta Gwamna Malam Ibrahim Shekarau, ta gudanar da zaben kananan hukumomin a shekarar 2004, da 2007, sai dai a wannan karon Gwamnatin Injiniya Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso za ta gudanar da zaben, bayan ta samu shekaru uku cur tana kan karagar mulki, duk wannan tsawon lokaci da ta yi tana tafiyar da Majalisun ne a karkashin jagorancin Kantomomin riko.
Wannan zabe na Jihar Kano, shi zai fitar da jihar daga cikin jerin jihohi 11, na kasar nan da suka yi watsi da zaben kananan hukumomi a jihohinsu, sauran jihohin 10, da har yanzu basu yi zaben ba. Jihohin sun hada da Katsina da Delta da Ekiti da Barno da Osun da Oyo da Abia da Bauchi da Imo da Ondo.
Hukumomin zaben jihohi sun yi kaurin sunan cewa ba wani mai cin zabe a zabubbukansu koda kuwa jama`a sun zabe shi, sai dan takarar jam`iyyar da ke mulkin jihar, al`amarin da ya saba wa tsarin tafarkin dimokuradiyya, wanda kuma kan haddasa rigingimun da kan kawo asarar rayuka da jikkata al`umma da bata dukiyoyinsu da na gwamnati. Don haka Hukumomin zaben jihohi ake yi musu lakabi da “Ka ci, ba ka ci ba, Ka ci,” Amma dai a wannan karon shugaban Hukumar zaben Jihar Kano, Dokta Sani Lawal Malumfashi ya sha alwashin cewa za su gudanar da zabubbukan cikin gaskiya da adalci, ya kara da bada tabbacin cewa ko kusa ba za su nuna son zuciya ba a cikin zabubbukan, don haka dukkan jam`iyyar da ta ci koda Kansila ne za a ba ta nasarar ta. Ko haka za ta samu, ko ba za ta samu ba, sai a lokacin zabe da bayan bayyana sakamakonsa za iya gasgata abin da ya fadi. Babu dai wani korafi dgame da hukumar zaben daga jam’iyyun da za su yi takara. Koke-koken kurewar lokaci na mika sunayen `yan takara da shugabannin jam`iyyun suka rika yi a baya ya sa Hukumar zaben ta ce don tabbatar da adalci ga jam`iyyun ya sanya ta kara musu wa`adin kwanaki uku, inda kowace ta samu sukunin mika jerin sunayen `yan takarar ta na shugabanni da kansiloli.
Idan mai karatu bai manta ba sakamakon zabubbukun Majalisun kananan hukumomi na karshe da Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta gudanar a shekarar 2007, sun bar baya da kura, wanda fadin sakamakonsu ya sanya aka yi ta kone-konen kaddarorin gwamnatin jihar da wasu Ofishoshin Majalisun kananan hukumomi a cikin birnin Kano da sauran sassan jihar, kone-konen da suka janyo asarar dukiyoyi na dubun-dubatar miliyoyin Naira. Wadancan tashe-tashen hankula za ka iya alakanta faruwarsu tun daga irin yadda aka yi kama karya cikin tsayar da `yan takarar da ba su jama`a suke so ba, musamman a cikin jam`iyyar ANPP, wadda ke mulkin jihar a zamanin, bisa ga kawai sanin da `yan takara suka yi cewa da zarar ka samu takara a jam`iyya mai mulki, to, kuwa ka ci zabe. Wasu daga cikin rikicinma an yi zargin daga cikin jam`iyyar `yan takarar da ba a tsayar ba suka taimaka wa `yan jam`iyyar adawa cikin rura wutarsa.
Ya kamata mai karatu ya sa ni cewa a yanzu din ma ba ta canja zane ba, don kuwa ana zargin cewa akasarin `yan takarar da jam`iyyar APC mai mulkin jihar ba su ne `yan jam`iyyar hadaka da ta haifar da APC din suke so ba, bisa la`akari da cewa `yan jam`iyyar PDP da ada ita ke mulkin jihar, amma dawowar Gwamna jihar, Dokta Kwankwaso cikin jam`iyyar hadakar ta APC, su suka fi samun daukaka cikin tsayar da `yan takarar na APC.
A gefe daya kuwa, canjin shekar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau daga jam`iyyarsu ta APC da suka kafa zuwa ta PDP, shi ma ya taimaka wajen canja yadda zaben zai kasance a jihar.
Ya zuwa yammacin Lahadin wannan makon an samu fadace-fadace siyasa har sau biyar dukkan su tsakanin magoya bayan jam`iyyar APC da na PDP, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu da jikkata wasu 12, a cikin yakin neman zaben da `yan takarar jam`iyyun biyu suke kai. Rundunar `yan sandar jihar ta tabbatar da afkuwar haka, inda ta ce an yi wadannan fadace-fadace ne a kananan hukumomin birnin Kano da kewaye da Rogo da Dala da Gezawa da Nassarawa. Daga cikin irin wadannan fadace-fadace da aka fara, wandanda zuwa yanzu jami`an tsaro da mutanen jiha, suke dora alhakin faruwarsu akan shugabanni da mabiyan jam`iyyun biyu, sai dai kawai mu yi ta addu`a a yi zabe lafiya, amma ba daga irin take-taken masu neman mulkin ba. Don haka sai mu ci gaba da addu`ar Allah Ya sa a yi zabe lafiya.