Fataucin yara: An kama wata mata da yara 15 a Fatakwal

Asirin wata mata mai suna Maureen Wechinwu mai kimanim shekara 44 a duniya, a lokacin da ta shiga komar jami’an tsaro Jihar Ribas, sakamakon kama ta da kanana yara sama da 15. An dai kama ta da yaran ne a gidanta da ke Aluu, yankin karamar hukumar Ikwerre ta jihar. ’Yan Hisbah sun kama mace […]

Fataucin yara: An kama wata mata da yara 15 a Fatakwal

wani yaro an rufe masa baki da hannu. (Hoto: Shutterstock)

Asirin wata mata mai suna Maureen Wechinwu mai kimanim shekara 44 a duniya, a lokacin da ta shiga komar jami’an tsaro Jihar Ribas, sakamakon kama ta da kanana yara sama da 15.

An dai kama ta da yaran ne a gidanta da ke Aluu, yankin karamar hukumar Ikwerre ta jihar.

Tun farko wadda ake zargin ta yi ikrarin cewa, ita babbar malamar cocin ‘Ladies of Victory’ ce wadda hedikwatarta ke Ingila kuma tana da gidan marayu ne a kasuwar Ogboro.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Ribas, Friday Ebola ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda ya bayyana cewa, rundunar Zaman Lafiya, wato Operation Restore Peace sun samu bayanan sirri, inda suka kai samame gidan matar.

Ya ce, “Bayanan sirri da muka samu ya nuna matar ta fake da sunan gidan marayu ta tara ’ya’yan mutane tana azabtar da su a layin OmuIgke da ke rukunin gidaje na 2 da a Aluu, inda aka same ta tare da yaran, aka kama ta da su kuma aka kubutar da su,” in ji Kwamishinan ‘Yan sanda Ebola.

Wadda ake zargi da tara yaran tana fataucinsu,ta shaida wa Aminiya cewa, “Tun da farko gidan marayu na bude, inda na fara tara yaran da mahaukata suka haifa daga bisani ne kuma wani mutum mai suna bictor ya rika kawo min yaran har gida, ya kai ga matsa min lamba ina ba shi kudi, wata rana Naira dubu 50,wata ranar kuma dubu 100 ya ke karba kan ko wane yaro ko yarinya da ya kawo min,” in ji ta.

Da aka tambaye ta ko yaya take yi da yaran ta kasa cewa uffan, amma ta dage kan cewa gidan marayu ne, inda daga bisani ta ce, “Na kunyata kaina da kuma al’umma ta, wannan abun kunya har ina.

Yaran dai kamar yadda wakilinmu ya samu bayani daga Rundunar ‘Yan sandan jihar, an yi musu dauki dai-dai ne daga sassan jihohin Kudu Maso Kudu.

Kwamishinan ’Yan sandan jihar ya ce, matar ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, kuma da zarar sun kammala bincike za su mika ta zuwa kotun don zartar mata da hukunci.