Faten masara ya hallaka mutum 8 a Zamfara
A ranar Larabar da ta gabata ce iyalin Namakaka da ke Unguwar Kwanar Umaru Shinkafi a karamar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara suka rasa mutum 8 daga cikinsu sanadiyar cin faten masara da matar gidan ta dafa. Bayan dahuwar abincin ne daukacin wadanda suka ci in ban da yaro daya da yake yi masu […]

A ranar Larabar da ta gabata ce iyalin Namakaka da ke Unguwar Kwanar Umaru Shinkafi a karamar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara suka rasa mutum 8 daga cikinsu sanadiyar cin faten masara da matar gidan ta dafa.
Bayan dahuwar abincin ne daukacin wadanda suka ci in ban da yaro daya da yake yi masu dibar ruwa a gidan suka rasu nan take har da matar gidan da ta dafa abincin.
Aminiya ta zanta da daya daga cikin iyalan gidan Malam Sanusi Bala wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Zuwa karfe 11 na safiyar Laraba aka bizne mamatan. Marigayiya Jummai ita ce ta dauko lawashin albasar da ta ajiye ta yanke ta hada shi da tsakin masara ta yi fate domin ci a gidan. ’Ya’yanta biyu Sa’adiyya da ta dade ba ta gidan tana wajen yayarta ta zo a yi mata kitson Sallah da Ibrahim da ’ya’yan abokiyar zamanta hudu Isah da Aliyu da Fati da Jamilu da kuma wata ’yar unguwar da ta zo daga makarantar boko mai suna Hafsa duk sun ci wannan faten kuma ya zama ajalinsu,” inji shi.
Ya ce wannan abu sun dauke shi a matsayin kaddara daga Allah ne, kuma ya ce asakarin matan da suka rasu ’yan mata ne in aka cire mahaifiyarsu. “Wannan abin ya zo da karar kwana tunda wani ya ci bai yi masa komai ba, amma su ne lokacinsu ya yi faten ya yi sanadi ne kawai cewa shi za su ci su bar duniya fatanmu Allah Ya gafarta musu Ya ba mu hankurin rashinsu,” inji shi.