Fati KK ta shirya wa ’yarta bikin cika shekara 2 da haihuwa
A ranar Juma’ar makon jiya ne fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fati KK ta shirya wa ’yarta Hafsat bikin cika shekara biyu da haihuwa a Kaduna.Bikin, wanda aka gudanar a dandalin taro na Habil da ke kan Titin Muhammadu Buhari, ya samu halatar ’yan fim kamar su: Nura MC da Ummi KD da mawaki Muhammad Bana […]
A ranar Juma’ar makon jiya ne fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fati KK ta shirya wa ’yarta Hafsat bikin cika shekara biyu da haihuwa a Kaduna.
Bikin, wanda aka gudanar a dandalin taro na Habil da ke kan Titin Muhammadu Buhari, ya samu halatar ’yan fim kamar su: Nura MC da Ummi KD da mawaki Muhammad Bana da dai sauransu.
Bayan mawaka sun nishadantar da mahalarta bikin da kade-kade da wake-wake ne, sai aka ci, aka sha, daga bisani kuma Hafsat ta yanka kek din bikin, wanda mahaifiyarta da sauran mahalarta suka rufa mata baya.
A karshe Fati ta yi godiya ga jama’a da suka halarci bikin tare da yi musu fatar komawa gidajensu lafiya.
Ga masoyanta kuma ta ba su tabbacin cewa tana tare da su a kowane lokaci.