Fatima Fouad Hashim: Dan hakin da ka raina…

Fatima Fouad Hashim na cikin matasan da ake damawa da su a kafofin zamani

Fatima Fouad Hashim: Dan hakin da ka raina…

Duk da kuruciyarta, Fatima Fouad Hashim na cikin masu fada a ji a soshiyal midiya

Fatima Fouad Hashim matashiya ce; amma ayyukan da ta yi, idan aka yi la’akari da yawan mutanen da ta sauyawa rayuwa, ko a tsakanin manya sai an tona.

Galibin mutanen da suka san Tauraruwar tamu ta yau, mai yiwuwa sun san ta ta hanyar shafukanta na sada zumunta da ake kira Open Diaries.

Open Diaries wurare ne da mutane ke zuwa idan suna da matasala ko damuwa domin a ba su shawara.

Ita da sauran ma’abota Open Diaries (wadanda wasunsu kwararru ne a fannonin rayuwa daban-daban) kan ba da shawara, kuma a samu maslaha.

Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda matashiya haka ke taimaka wa mutane warware matsalolinsu na rayuwa – kama daga aure zuwa ga abota da sauran batutuwa na rayuwa.

Zumunci a kafa yake

Ganin yadda Open Diaries ke taimaka musu, wasu ma’abota shafukan suka samar da wata al’umma.

Da yake an ce zumunci a kafa yake, Fatima ta yanke shawarar bunkasa ayyukanta daga shafukan sada zumunta zuwa unguwanni da garuruwa da ma jihohin Najeriya don baya da tallafi.

Gidauniyarta ta Open Diaries ta samar da tallafin abinci da sutura ga mabukata, ta gina rijiyoyin burtsatse, ta biya wa masu karamin karfi kudin asibiti, ta kuma biya wa dalibai marasa galihu kudin makaranta a jihohi.

Zuwa yanzu gidauniyar ta yi aiki a jihohin Najeriya 10.

Sannan kuma Fatima Fouad Hashim ta koyar da mata fiye da 100 sana’o’i daban-daban da nufin karfafa su su dogara da kansu.

Tauraruwar tamu ta yau ta yi digirinta na farko ne a fannin Akanta a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan tana kan karatun digiri na biyu a fannin a Jami’ar ta Bayero.

Haka kuma ta dauki hanyar kwarewa a aikin Akanta tare da Cibiyar Kwararrun Akantoci ta Najeriya (ICAN).

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos