Fatima Paga na shirin kafa tarihi a Yobe
A lokacin da ake ta shirye shiryen fara tunkarar zaben 2019, Mazabar Bade ta Yamma a Jihar Yobe na shirin kafa tarihi, inda a karon farko al’ummar yankin suka fitar da mace ta farko da za ta fara gwada sa’arta a zaben majalisar dokokin jihar da a tarihi mace ba ta taba yin takara ba, […]

A lokacin da ake ta shirye shiryen fara tunkarar zaben 2019, Mazabar Bade ta Yamma a Jihar Yobe na shirin kafa tarihi, inda a karon farko al’ummar yankin suka fitar da mace ta farko da za ta fara gwada sa’arta a zaben majalisar dokokin jihar da a tarihi mace ba ta taba yin takara ba, balle ta zama ‘yar majalisa.
Da yake bayyana dalilansu na yin kira ga Fatima Paga, da ta fito musu takara, Abubakar Musa Paga, wanda shi ne babban daraktan yakin neman zaben nata, cewa ya yi halayenta nagari ne suka sanya suka bukaci ta zama wakiliyarsu a majalisar jihar.
“Fatima mutum ce mai kokari akan jama’arta tun tale-tale, shi yasa muka ce ta fito dan mun san tallanta ba zai mana wahala ba. Sannan ita ce ta fi kowanne dan takara cancantar mu zabe shi a 2019,” in ji Paga.
Shi ma Ibrahim Dogona, cewa ya yi suna tare da Fatima dari bisa dari ta zama musu ‘yar majalisa saboda matashiya ce mai jini a jika da suke jin ba za ta kunyata su ba. Ya kara da cewa a Mazabar Bade ta Yamma akwai matsaloli sosai wadanda idan ba Fatima ce za ta wakilce su a majalisa ba, suna ganin za a dade ba a shawo kan matsalolin ba domin an bar su a baya.
Haka zalika shi ma shugaban zauren matasa na Bade ta Yamma, Sani Helma cewa ya yi Fatima mace ce jaruma mai kamar maza wacce idan Allah Ya ba ta majalisa duk wani dan Mazabar Bade zai ji dadi shi yasa su suka nemi sai ta fito takara. Sani Helma, ya kuma ce tun shekarar 1999 maza ke jagoranci amma babu abin da suka tsinana musu, amma ganin ita Fatima Paga tana aiki ne a Damaturu amma take zuwa har yankinta ta taimaka mana, shi yasa muke ganin za ta kasance mai adalci idan ta zama ‘yar majalisa.
Da Aminiya ta tuntubi ita Fatima Paga, dan jin ko ta amince za ta amsa kiran jama’ar na ta sai ta ce a lokacin da jama’ar suka zo ma ta da batun ba ta ce komai ba sanda ta tuntubi iyayen gidanta a ciki da wajen jihar Yobe dan samun shawarwari, sannan ta amince da kiran da aka mata.
Fatima Paga, ta ce in Allah Ya yarda kamar yadda aka nemi ta tsaya dan kafa tarihi na kasancewar ta mace ta farko da za ta fara kafa tarihi na fitowa takarar kujerar ‘yar majalisar jiha idan ta ci zabe za ta bada mamaki. “gwamnatin Alhaji ibrahim Gaidam gwamnati ce mai damawa da matasa da mata baki daya kuma kusan kashi sittin na manufofinta biyawa mata da matasan ne bukatarsu kamar ta fannin ilimi da kiwon lafiya da ma noma da samar da sana’oi domin dogaro da kan su,” in ji ta.