Fatima Zahra Umar: Tsaro hujja daga kotu zuwa kafofin sadarwa
Fatima Zahra Umar sananniya ce wajen gwagwarmayar ganin mata sun samu ta-cewa
Barista Fatima Zahra Umar lauya ce, amma daga bisani ta tsunduma harkar yada labarai, musamman a bangaren wayar da kan mata.
Da farko dai ta kirkiro wani shafin intanet (blog) mai suna Divorce Diaries wanda yake duba a kan yadda aurarraki ke durkushewa.
- Tauraruwar Arewa: Watan girmama matan Arewa ya tsaya
- Dokta Mariya Bunkure: Fafutuka wajen sama wa mata ilimi tun daga tushe
Da yake an ce ga na gaba akan ga zurfin ruwa, shafin na yin nazari a kan wannan lamari ne da nufin gano ummulhaba’isun mutuwar auren ko wasu sa dauki darasi.
Bayan nan, ta hada gwiwa wajen kirkiro mujallar intanet ta “Jaruma” ta kuma zama Babbar Editar mujallar.
Muryar matasa
Wannan mujalla ta taka muhimmiyar rawa wajen fitowa fili da batutuwan da ke da muhimmanci ga mata, da ba su shawarwari a kan yadda za su bayar da gudunmawa wajen ciyar da al’umma gaba.
Tauraruwar tamu ta kuma gabatar da Shirin “Adikon Zamani” a Sashen Hausa na BBC, inda take tattauna wasu batutuwa da suka shafi mata wadanda ba kasafai ake magana a kansu ba.
Ta hanyar sirin, Fatima Zahra Umar ta taimaka wajen wayar da kan mata game da wasu muhimman abubuwan da ba su fahimce su ba, amma wasu dalilai suka hana su neman karin bayani.
Sannan kuma ta yi fice a fagen fafutukar ganin ana damawa da mata da matasa a harkokin siyasa.
Mai yiwuwa ma matukar sha’awar da take da ita ta ganin matasa sun shiga an yi da su ne ya sa take da burin zaman Gwamna watan wata rana.
Abar koyi a Arewa
A shekarun 2016 da 2017, Fatima Zahra Umar ta shiga cikin jerin matasa 100 masu karfin fada a ji a Arewa.
A shekarar 2018 kuma ta shiga cikin mata matasa kalilan da aka saka a cikin Kwamitin Shirya Babban Taron jam’iyyar APC na Kasa da Kwamitin Shirya Zaben Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar.
A yanzu haka, Tauraruwar tamu tana aiki ne a Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa a matsayin mataimakiya ta musamman a kan al’amuran da suka shafi mata.