Fayose bai amince da tuhumar da ake yi masa ba
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose a jiya bayan da babbar kotun jihar Legas take tuhumarsa da laifuka da barnatar dukiyar jihar da ya kai sama da naira biliyan 30, amma Fayose bai amince da tuhumar da ake yi masa ba. Ana dai tuhumar tsohon Gwamnan ne tare da kamfaninsa na Spotless Investment Limited wanda […]
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose a jiya bayan da babbar kotun jihar Legas take tuhumarsa da laifuka da barnatar dukiyar jihar da ya kai sama da naira biliyan 30, amma Fayose bai amince da tuhumar da ake yi masa ba.
Ana dai tuhumar tsohon Gwamnan ne tare da kamfaninsa na Spotless Investment Limited wanda Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta gurfanar da shi akan laifukan da ya aikata lokacin yana Gwamnan jihar Ekiti.
Alkalin kotun Mojisola Olatiregun ya bada umarnin a ci gaba da tsare Fayose a hannun EFCC har zuwa gobe Laraba, lokacin da kotun zata iya bada belinsa.