FCE Gombe za ta koma karatu ranar 9 ga Nuwamba

Kwalejin ta ce ta tanadi duk abin da ake bukata na kariya daga cutar COVID-19

FCE Gombe za ta koma karatu ranar 9 ga Nuwamba

Hukumar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FCE) da ke Gombe, ta ce za ta ci gaba da darussa daga ranar Litinin, 10 ga Nuwamban da muke ciki.

Magatakardar kwalejin, Umar Muhammad Bello, ya umarci dalibai masu neman takardar shaidar malanta (NCE) da sauran dalibai da malaman kwalejin da su koma don ci gaba da karatu.

Hukumar makarantar ta ce, ta yanke shawarar ci gaba da karatu ne bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na bude kwalejojin ilimi.

Sanarwar ta ce, babu dalibin da za a bari ya shiga cikin makarantar ba tare da ya cika dokokin kare yaduwar cutar COVID-19 da hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar ba.

Ta ce kafin komawa makarantar, hukumar kwalejin ta dauki dukkannin matakan kare dalibai da malamai daga cutuka masu yaduwa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos