Ficewar Atiku APC: Gwamna Bindow da Maman Taraba na nan daram

Gwamnan Jihar Adamawa, Muhammed Umar Jibrilla Bindow, ya ce ba zai bi sahun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wurin ficewa daga jam’iyyar APC ba. Ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talatar da ta gabata a fadar shugaban kasan, inda ya ce zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC […]

Ficewar Atiku APC: Gwamna Bindow da Maman Taraba na nan daram

Gwamnan Jihar Adamawa, Muhammed Umar Jibrilla Bindow, ya ce ba zai bi sahun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wurin ficewa daga jam’iyyar APC ba.

Ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talatar da ta gabata a fadar shugaban kasan, inda ya ce zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC har tsawon rayuwarsa don haka ya ce ba shi da niyyar yin biyayya ga Atiku Abubakar ta ficewa daga jam’iyyar. “Saboda haka ni dan Jam’iyyar APC ne har tsawon rayuwata,” in ji shi. 

Haka ita ma Ministar Mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan (Maman Tara) wata majiya ta tabbatar da cewa ta jaddada biyayyarta ga Shugaba Buhari ranar Talatar a ofinshinsa, inda ta ce tana nan daram a Jam’iyyar APC babu inda zata je. Koda yake ministar ta ki cewa uffan game da ficewar mai gidan nata Alhaji Atiku Abubakar daga jam’iyyar ta APC da kuma abinda ya gudana tsakaninta da shugaban kasar.

Majiyar ta ci gaba da cewa, Ministar ta tabbatar wa shugaban kasa cewa tana tare da shi, kuma zai samu goyon bayanta a 2019, sannan ta jadda masa cewa ba zata bi Atiku Abubkar zuwa wata jam’iyya ba. Haka kuma wakilin Daily Trust ya yi kokarin jin ta bakinta amma lamarin ya ci tura, domin ba ta dauki waya ba, kamar yadda ba ta maida jawabin sakon da aka aike mata ba.   

A makon jiya ne Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar, yana mai zarginta da rashin cika alkawuran da ta yi wa al’ummar kasar da kuma tabbatar da dimokuradiyyar cikin gida.

Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman-zamansa jagororin jam’iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam’iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam’iyyarsa ta PDP. Ya ce ce an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba.

“A kan wannan dalili ne mambobin jam’iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin bin kundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci. A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam’iyyar a watan Faburairun 2014, don a lokacin ba ni da jam’iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni,” a cewar sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa: “Duk jam’iyyar da ba za ta kula da al’amuran matasa ba, to matacciyar jam’iyya ce. Domin makomar kasar nan tana hannun matasa ne.” Koda yake kawo lokacin hada wannan rahoto Atiku Abubakar bai aiyana jam’iyyar da zai shiga ba, sannan dan siyasa da a baya sha sauye-sauyen jam’iyya.