Ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai na ci gaba da jawo rudani
Ga dukkan alamu ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai sakamakon kuri’ar raba-gardamar da aka gudanar a makon jiya na jawo rudu a tsakanin jama’ar kasar da kuma na wasu yankuna da suka tada kasar.Babbar Ministar yankin Scotland da ke kasar ta Birtaniya Misis Nicola Sturgeon ta je Brussels don bayyana niyyar yankin na ci gaba […]
Ga dukkan alamu ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai sakamakon kuri’ar raba-gardamar da aka gudanar a makon jiya na jawo rudu a tsakanin jama’ar kasar da kuma na wasu yankuna da suka tada kasar.
Babbar Ministar yankin Scotland da ke kasar ta Birtaniya Misis Nicola Sturgeon ta je Brussels don bayyana niyyar yankin na ci gaba da zama cikin kungiyar Tarayyar Turai bayan kuri’ar janyewa da Birtaniya. Sturgeon ta ce a shirye take ta kare martabar Scotland bayan ta bukaci gudanar da zaman majalisa na musamman don ba ta goyon bayan zuwa tattaunawa da kungiyar.
Kashi 62 na masu zabe daga Scotland sun zabi ci gaba da zama cikin kungiyar Tarayyar Turai.
Sai dai Magajin Garin Birnin Landan, Sadik Khan ya ki amincewa da bukatar ballewa daga Birtaniya da wasu ke kira a kai, bayan zaben raba-gardamar da ya tabbatar da ficewar kasar daga cikin kungiyar.
Amma Magajin Garin ya bukaci a bai wa birnin kujera ta musamman a tattaunawar da za a yi tsakanin Birtaniya da wakilan kungiyar Tarayyar Turai. Kuma ya bukaci bai wa Landan karin karfin gudanar da ayyuka da suka hada da kashe kudi.
Zuwan Misis Nicola Sturgeon birnin Brussel ya zo daidai da zuwan Firayi Ministan Biritaniya Mista Dabid Cameron da ya ce zai gana da shugabannin kasashen Turai a kan tasirin ficewar Biritaniya daga kungiyar da kuma nemo mafita.
A ranar Litinin shugabannin kasashen Jamus da Faransa da Italiya sun ce babu wata tattaunawa da za su yi a kan fitar Biritaniya daga kungiyar.
Gidan rediyon BBC, ya ruwaito Sakataren Lafiya na Biritaniya, Jeremy Hunt yana kiran a gudanar da zaben raba-gardama karo na biyu na sharuddan fitar kasar daga Tarayyar Turai. Ya ce, ya kamata a jinkirta fita daga Tarayyar Turai har sai bayan zaben kasar da za a yi a shekarar 2022, kuma shi ne babban jami’in gwamnatin Birtaniya na farko da ya fito fili ya yi wannan kira.