Ficewar Isa Yuguda daga PDP alheri ne gare ta – Nuhu Zaki
A ranar Asabar din makon shekaranjiya ne tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya kira taron manema labarai ta waya inda ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar PDP. Bayan samun wannan labara Aminiya: Farko za mu so ka gabatar da kanka?Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki, kamar yadda kuka sani sunana Abdulrazak Nuhu […]
A ranar Asabar din makon shekaranjiya ne tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya kira taron manema labarai ta waya inda ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar PDP. Bayan samun wannan labara Aminiya: Farko za mu so ka gabatar da kanka?
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki, kamar yadda kuka sani sunana Abdulrazak Nuhu Zaki, tsohon kansila tsohon Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Warji, tsohon shugaban karamar hukumar a karshe dan Majalisar Wakilai. Tun lokacin da aka dawo mulkin farar hula a 1999 nake tsayawa takara kuma mutanena suna zaba ta saboda alaka mai kyau a tsakanina da su, mun taimaka a fannonin kiwon lafiya da samar wa matasa aiki da bunkasa noma da kiwo tallafa wa jama’a da sauransu.
Mun amince da kayen da aka yi mana a zaben shekara ta 2015, kuma muna fatar za mu sake kafa sabuwar gwamnati a zaben shekara ta 2019 in Allah Ya yarda. Akwai wani lokaci da muka zauna da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da sauran masu ruwa-da-tsaki a PDP, ni na tashi na fada wa shugaba Jonathan cewa kai ne matsalar PDP, tsakani da Allah idan za ka yi hakuri da takara, PDP za ta kai labari a shekarar 2015. Na yi takara a 2015 amma duk inda na je nakan fada wa mutane cewa za a zabe mu amma ban da kai, saboda haka abin da na fada shi ne ya tabbata a 2015. Ina daya daga cikin ’yan siyasa masu akida amma ba za ka fahimci haka ba sai ka je mazabata, za su ba ka labari duk abin da al’umma ke bukata shi ne abin da nake so.
Mene ne ra’ayinka game da matakin da tsohon Gwamna Isa Yuguda ya dauka na ficewa daga PDP?
Tabbas tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya fada wa duniya cewa ya fice daga tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP saboda kazantarta. Ban yi mamakin matakin da ya dauka ba, domin tun kwanakin baya na fahimci cewa zai yi wahala ya ci gaba da zama a PDP. Ina daya daga cikin na hannun damar Malam Isa Yuguda, amma abin da ban yarda da shi ba, shi ne hassada a siyasa. Babban damuwarsa ita ce ba zai yi siyasa da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu da tsohon Ministan Abuja Sanata Bala Muhammed da Sanata Abdul Ningi da tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Abdulmalik Mahmoud ba. Wadannan mutane su ne kazamai a wurinsa saboda haka ko a kore su daga PDP ko kuma ya fice daga jam’iyyar ta PDP. Jam’iyya kasuwa ce kowa da abin da yake kawo shi, to amma matakin da ya dauka bai yi adalci ga magoya bayansa ba. Ya kira mu inda ya bayyana cewa matukar ba za a kori wadancan mutane ba, to tabbas zamansa a PDP ba ya da wani amfani. Don haka ya kira taron manema labarai ya sanar da cewa ya fice daga PDP. Ficewarsa daga PDP alheri ne domin yanzu ne PDP za ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Bauchi, mun fada masa cewa ba za mu fita daga PDP ba muna nan daram. Ya kamata Malam Isa Yuguda ya fahimci cewa tun 1999 muke PDP, kuma ba za mu fice daga PDP domin mu ba kazamai ba ne kamar yadda yake ci gaba da fadi.
Ba ka ganin ficewarsa a PDP zai yi mata illa?
Ina tabbatar maka da cewa babu wata illa da ficewarsa za ta haifar wa PDP, domin duk wanda yake gadara da su suna nan a PDP har gobe mun samu labari akwai wasu daga cikin tsofaffin kwamishinoninsa sun bi shi kuma muna yi musu fatar a sauka lafiya. Ni dan siyasa ne kuma ni ba yaron wani ba ne a siyasance, abin da kullum na sa a gaba shi ne yarda da kaddara mai kyau ko mummuna kuma na wuce in yi siyasar ubangida. Tun daga kansila na fara takara har zuwa matsayin da na rike na karshe dan Majalisar Wakilai, don haka na san abubuwan da ke tafiya tun daga matakin gunduma har zuwa jiha da kananan hukumomi da kasa baki daya.
Yanzu za mu iya cewa PDP za ta samu zaman lafiya a Bauchi ke nan?
Ina tabbatar maka cewa yanzu PDP za ta samu zaman lafiya tunda ya fice daga cikinta, kuma za ta sake karfi. Fitarsa alheri ce ga PDP da magoya bayanta, muna fatar Allah Ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Mene ne sakonka ga ’yan siyasan Jihar Bauchi?
Babban sakona ga dillalan ’yan siyasa na Jihar Bauchi shi ne fitar Malam Isa Yuguda daga PDP zai zamo musu alheri, domin an fara samun rudami a cikin wasu magoya bayansa tun lokacin da ya samu labarin cewa an daidaita bangarori biyu na PDP da ke rikici an yi sulhu sai ya dauki matakin fita daga jam’iyyar.
Ina tabbatar maka cewa ko gobe aka sake zabe PDP ce za ta kafa gwamnati a Jihar Bauchi, ko yanzu manuniya ta nuna domin shugabannin PDP suna da tausayi da alheri ga mutanen mazabunsu. Kuma babu wani dan siyasa a Najeriya da zai sake shiga rigar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaudari mutane ya ci zabe. Kowa zai ji da kansa ne babu wanda zai sake yin sak a siyasance akwai mutanen kirki a PDP haka kuma akwai mutanen kirki a APC.
Mene ne sakonka ga mambobin Jam’iyyar PDP na jihar?
Babban sakona ga magoya bayan PDP shi ne su kwantar da hankalinsu, Malam Isa Yuguda ba ya ba da mulki sannan kuma ba ya hana mulki. Allah ne Yake ba da shugabanci ga wanda Ya so, Allah ke wadata dan Adam ba wani mutum ba. Malam Isa Yuguda ya same ni a PDP daga bisani ya sauya sheka zuwa ANPP kuma ya sake dawo PDP ya same mu daram na riga shi shiga siyasa. Farin jininsa a siyasance a shekarar 2007 ya sha bamban da shekarar 2015. Na yi mamakin abubuwan da ya fada a taron manema labarai da ya kira. A zaben shekarar 2015 da kansa yake fada cewa dole sai an zabi Jonathan, mun fada masa cewa babu ruwansa da maganar zaben Jonathan kowa ya zabi abin da yake so amma ya ki amincewa. Ban zabi Jonathan ba a matsayina na tsohon dan Majalisar Wakilai domin bai cancanta ba, mutanen mazabata sun fada min cewa ba sa son Jonathan kuma ba za su zabe shi ba.
Me za ka ce game da rikita-rikitar kasafin kudin 2016?
Ya kamata al’umma su fahimci cewa akwai kura-kurai ne a kasafin kudin, don haka ’yan majalisa suka ce dole a sake lale. Amma ba kowa ne zai fahimci haka ba sai wanda ya yi aiki a matsayin dan majalisa ko sanata. Sanata danjuma Goje shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi, akwai wasu kura-kurai ne da suka gano suke kokarin gyara amma saboda son zuciya na wadansu mutane suke ci gaba da sukarsu ta kafafen watsa labarai. Akwai wuraren da dole sai sun gudanar da wasu gyare-gyare saboda haka muna kira ga al’umma su gane cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da dama ga Shugaban kasa ya fara aiwatar da kasafin kudi kafin majalisa ta amince. Akwai wasu da ba sa goyon bayan shugabannin majalisar don haka suke kokarin shafa musu kashin kaji saboda haka ya kamata wadanda suke kusa da Shugaban kasa da suke neman haddasa fitina a majalisa su yi hakuri su bar ’yan majalisa su ci gaba da gudanar da ayyukansu. Muna ganin (zargin) Bola Ahmed Tinubu na daya daga cikin wadanda suke haddasa fitina a wannan gwamnati, amma ya kamata su koyi darasi daga abin da ya faru da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal. Wannan takaddama babu wata matsala da za ta haifar ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda haka muna fatar masu neman haddasa fitina a majalisa su fahimci cewa dole a bar ’yan majalisa su gudanar da aikinsu ba tare da wata matsala ba.