FIFA ta amince da yin amfani da dan kwali da rawani a lokacin kwallo a Pakistan da Afghanistan

Jami’an hukumomin da ke shirya wasan kwallo a garuruwan Pakistan da na Afghanistan sun nuna farin cikinsu a kan dage dokar hana amfani da dan kwali da kuma rawani a lokacin kwallo a garuruwan Larabawa musamman a garin Pakistan da kuma na Afghanistan da Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi a ranar Asabar […]

FIFA ta amince da yin amfani da dan kwali da rawani a lokacin kwallo a Pakistan da Afghanistan

AFTER ALI KNOCKS LISTON TO THE FLOOR HE SHOUTS ‘GET UP AND FIGHT, SUCKER.’ THERE IS SOME CONFUSION ABOUT WHEN THE THE COUNT FOR LISTON BEING DOWN IS STARTED.

Jami’an hukumomin da ke shirya wasan kwallo a garuruwan Pakistan da na Afghanistan sun nuna farin cikinsu a kan dage dokar hana amfani da dan kwali da kuma rawani a lokacin kwallo a garuruwan Larabawa musamman a garin Pakistan da kuma na Afghanistan da Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi a ranar Asabar da ta wuce.
Jami’an sun ce daukar wannan mataki ko shakka babu zai karfafa wa mata da maza da ke kasashen gwiwar cigaba da shiga harkar wasan kwallo ana damawa da su.
A ranar Asabar da ta wuce ne dai Hukumar ta amince wa mata amfani da dan kwali yayin da su kuma maza ta amince musu amfani da rawani a lokacin buga kwallo .
Rukhsana Rashid, kyaftin din kulob din mata na Dia da ke Pakistan ta nuna farin cikinta a kan haka, kuma ta ce hakan zai sanya mata da yawa su rungumi  harkar kwallo a kasar da kuma a daukacin Daular Larabawa.
“Ina mika jinjinta ga Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a bisa wannan mataki da ta dauka, don zai ba matan da iyayensu suka hana su fita ba tare da lullubi ba rungumar harkar kwallo a kasashen Larabawa”, inji ta.
Ita kuwa sakatariyar kungiyar kwallon kafa ta mata mai suna Sindhs a garin Pakistan mai suna Saadia Shaikh ta ce “matan da suka fito daga yankunan kasashen Larabawa za su yi murna da wannan mataki”.
Idan za a tuna a shekarar 2005 ce tsohon Shugaban kasar Pakistan Perbez Musharraf ya kirkiro  gasar wasan kwallon kafa na mata.
Ya zuwa wannan lokaci, Pakistan ta dauki nauyin gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na mata daban-daban har sau tara.  Sannan kasar tana da kungiyoyin kwallon kafa na mata guda 22 yayin da take da ’yan kwallon kafa mata fiye da 400.