FIFA ta bayyana kasashen da za su shirya gasar cin kofin duniya ta 2030

Hukumar ta ce za a yi gasar ce a kasashen Marocco da Spain da Portugal

FIFA ta bayyana kasashen da za su shirya gasar cin kofin duniya ta 2030

Shugaban FIFA

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta sanar da kasashen Marocco da Portugal da Spain cewa su za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2030.

Sai dai FIFA ta ce za a yi wasanni uku na farkon gasar a kasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay albarkacin cika shekara 100 cif-cif da fara gasar a lokacin.

Sanarwar wacce hukumar ta yi a ranar Laraba na nufin cewa za a gudanar da gasar ce a kasashe shida da ke nahiyoyi uku.

“FIFA ta amince da murya daya cewa za a gudanar da gasar ce ta hadin gwiwa a kasashen Morocco, Portugal da Spain a shekara ta 2023,” kamar yadda FIFA ta bayyana a cikin sanarwar.

“Bugu da kari, “la’akari da tarihin gasar da aka fara gudanarwa ta cin kofin duniya, hukumar gudanarwar FIFA ta kuma amince da murya daya cewa za a buga wasanni ukun farko na gasar a kasashen Uruguay, Argentina da Paraguay.”