FIFA ta ce za a gudanar da Gasar Kofin Duniya duk da rikicin Iran
Iran tana son a sauya wuraren wasanninta daga Amurka zuwa sauran ƙasashen da za su karɓi bakuncin gasar, wato Canada ko Mexico.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta jaddada cewa za a ci gaba da shirye-shiryen gudanar da Gasar Kofin Duniya ta 2026 kamar yadda aka tsara, duk da rashin tabbas kan halartar Iran.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino ne ya bayyana hakan a yayin taron majalisar hukumar da aka gudanar ta yanar gizo, inda ya ce hukumar na sa ran dukkan ƙasashe 48 za su halarci gasar cikin adalci da mutunta juna.
- An kwantar da jarumin fina-finan Amurka Chuck Norris a asibiti
- HOTUNA: Yadda Musulmi ke gudanar da bikin Sallah a sassan Najeriya
Sai dai halartar Iran na fuskantar shakku sakamakon yaƙin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya, musamman rikicin da ya shafi Amurka da Isra’ila.
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran, Mehdi Taj, ya nuna cewa ƙasar na shirin halartar gasar, amma tana son a sauya wuraren wasanninta daga Amurka zuwa sauran ƙasashen da za su karɓi bakuncin gasar, wato Canada ko Mexico.
Ya ce Iran na iya ƙaurace wa buga wasa a Amurka, amma ba za ta janye daga gasar baki ɗaya ba.
Haka kuma, shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta bayyana cewa ƙasarta a shirye take ta karɓi baƙuncin wasannin Iran idan buƙatar hakan ta taso.
Infantino ya ƙara da cewa duk da cewa FIFA ba za ta iya warware rikice-rikicen siyasar duniya ba, amma tana fatan amfani da ƙwallon ƙafa wajen haɗa kan al’umma da inganta zaman lafiya.