FIFA ta dakatar da Rasha daga buga kofin duniya na 2022
Matakin ya kuma shafi dukkan kungiyoyin kasar da ke buga kowace gasa.
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) da dakatar da kasar Rasha daga buga kowace irin gasa ta kasa da kasa, ciki har da gasar cin kofin duniya ta 2022, har sai abin da hali ya yi.
Matakin na zuwa ne bayan dakarun kasar Rasha suka mamaye Ukraine.
- Mahaifiyar Dokta Bashir Aliyu Umar ta rasu
- ’Yan ta’adda sun dasa bom a makarantu da asibitocin Kaduna
FIFA a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ta fitar ranar Litinin tare da twakwararta ta kasashen Turai (UEFA), sun kuma ce daga yanzu ba za a kyale kungiyoyin kasar su buga kowane irin wasa ba.
Hakan dai na nufin tawagar kungiyar kasar da za ta buga wasan neman shiga kofin duniya da za a yi a kasar Qatar, yayin da tawagar kungiyar matansu ta cancanta ta shiga gasar zakarun Turai da za a yi a watan Yuli mai zuwa.
Matakin ya kuma shafi kungiyoyin kasar ta Rasha da ke buga wasanni a gasa daban-daban a kasashen Turai.
“FIFA da UEFA a yau sun yanke shawarar cewa dukkan kungiyoyin Rasha, ko dai na kasa ko kuma na kulob-kulob, za a dakatar da su daga buga kowane irin wasa na FIFA ko na UEFA, har sai abin da hali ya yi,” inji sanarwar.
Gabanin wannan matakin dai, an tsara tawagar Rasha za ta buga wasa da kasar Poland ranar 24 ga watan Maris, kuma akwai yiwuwar ta fuskanci Sweeden ko Jamhuriyar Czech ranar 29 ga watan Maris.
Matakin na hukumomin kwallon kafar biyu na zuwa ne kwana daya bayan da farko sun yanke hukuncin cewa kungiyoyin kasar za su ci gaba da buga wasanni da sunan kasar, sannan ba tare da ’yan kallo ba.
Kazalika, FIFA ta kuma an haramta kunna taken kasar ko daga tutarta a filayen wasanni.
Sai dai sabon matakin na nufin yanzu kasar ko kungiyoyinta ba za su sake buga kowane irin wasa ba, har zuwa abin da hali ya yi.