FIFA ta dakatar da Shugaban Kwallon Kafar Sifaniya kan sumbatar ’yar wasa

Sumbatar Jenni Hermoso da Rubiales ya yi a leɓenta ya janyo cece-kuce.

FIFA ta dakatar da Shugaban Kwallon Kafar Sifaniya kan sumbatar ’yar wasa

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ta dakatar da Luis Rubiales daga matsayinsa na Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Sifaniya kan sumbatar ’yar wasan ƙwallon ƙafar ƙasar.

FIFA ta dakatar da Mista Rubiales daga shiga harkokin ƙwallon ƙafar a ƙasar da ma matakin duniya baki ɗaya.

Sumbatar Jenni Hermoso da Rubiales ya yi a leɓenta bayan da Sifaniya ta doke Ingila a wasan ƙarshe na Kofin Duniya na Mata ya janyo ce-ce-ku-ce mai zafi a duniyar wasannin.

A bayan nan an riƙa kiraye-kirayen Rubiales ya sauka daga muƙaminsa sakamakon sumbatar Hermoso.

To sai dai ya ƙi yin murabus yana mai cewa ya aikata hakan ne a cikin murna, don haka bai ɗauke shi a matsayin wani abu ba.

A ranar Alhamis ne FIFA ta buɗe bincike a hukumance kan Mista Rubiales mai shekarar 46.

Tun da farko dai ya riƙe gabansa a lokacin da ake murnar kammala wasan.

Rubiales ya nemi gafara ranar Litinin kan sumbatar ’yar wasan kafin FIFA ta buɗe bincike a kansa.

A ranar Juma’ar ya nemi afuwa kan cewa ya riƙe gabansa ne a lokacin da yake murna a bangaren VIP na filin wasan Sydney, yayin da Sarauniya Letizia ta Sifaniya da ’yarta mai shekara 16 ke tsaye kusa da shi.

Daga farko dai ya nemi kare kansa daga abin da ya aikata, yana mai cewa ya yi ƙoƙarin jajanta wa Hermoso ne bayan golan Ingila Mary Earps ta kama fanaretin da ta buga.