FIFA za ta inganta kwallon kafar mata a Saudiyya
Infantino ya ziyarci Saudiyya kan bunkasa kwallon kafar mata a kasar.
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) za ta taimaka wa kasar Saudiyya wurin inganta harkar wasan kwallon kafar mata a kasar.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino ya bayyana hakan yayin ganawarsa da jami’an Sashen Kwallon Kafar Mata na Hukumar Kwallon Kafa ta Saudiyya (SAFF) a lokacin da ya ziyarci kasar.
- Ko da a shirin fim mutum ya saki matarsa ta saku — Dokta Bashir
- Saki a fim: Yadda fatawar Dokta Bashir ta tayar da kura
- ’Ya ta kai karar mahaifinta ya yi mata ciki
- Kotu ta yanke wa soja hukuncin kisa ta haryar harbi
Infantino ya kai ziyarar ce tare da Mataimakin Babban Sakataren FIFA Football Mattias Grafström.
A ziyarar tasu, shugabannin na FIFA sun gana da Ministan Wasannin Saudiyya, Yarima Abdulaziz bin Turki Al-Faisal da shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar (SAFF), Yasser bin Hassan Al-Misehal.
Sun kuma gana da jami’an hukumar da kuma ’yan wasa, inda suka jaddada muhimman ayyukan da Saudiyya ke yi na bunkasa kwallon kafar mata daidai da tsarin hukumar.