Fikhun Soyayyar Ma’aurata
Assalamu alaikum wa rahmatullah! Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ina fata Allah (SWT) Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. Muna nan dai a bayani kan ilmin soyayyar ma’aurata, inda a yau za mu tattauna kan fikhun soyayyar ma’aurata, wanda zai nuna yadda soyayya take a shari’ance, da […]
Assalamu alaikum wa rahmatullah! Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ina fata Allah (SWT) Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin.
Muna nan dai a bayani kan ilmin soyayyar ma’aurata, inda a yau za mu tattauna kan fikhun soyayyar ma’aurata, wanda zai nuna yadda soyayya take a shari’ance, da fatan Allah Ya sa bayanin ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya zan ya amfanar da su.
Hukuncin Soyayyar Ma’aurata A Shari’a
In muka bibiyi da yawa daga cikin ayoyin Alkur’ani da kuma Hadisan Manzon rahma, (Sallallahu Alaihi Wasallam -SAW), da labaran magabatanmu, Allah Ya kara yarda a gare su, za mu fahimci cewa yana daga cikin kyautatuwa, inganta da cikar kamalar mutum ya kasance mai soyayya ne, mai kuma bayyanar da soyayyarshi ga abin da yake so. Ba wani waje da addini ya yi hani ga soyayya ko bayyanar da ita, sai dai ma a wurare da yawa an nuna yin hakan abin so ne kuma abin yabawa. Kalmar Soyayya ayar Alkur’ani ce, kuma Hadisan Manzon Allah cike suke da kyawawan misalai da ayyukan soyayya da kauna.
Soyayya A Alkur’anil Karim
Kalmar soyayya ko kauna sun bayyana a wurare 90 cikin Alkur’ani Mai girma, amma abin sha’awar shi ne, a duk inda suka bayyana suna bayani ne a kan sakamakon da ke bin soyayya, watau shi ne riko ga abin da ake so din. A kan haka muna iya fahimtar cewa duk wata soyayyar da ba riko kyakkyawa a cikinta, to ba za ta yi alfanu ba.
A aya ta 21 cikin Suratul Rum, Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana mana cewa Shi ne Mai sa soyayya a tsakanin mata da miji ma’auratan juna: “Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kawunanku, domin ku natsu zuwa gare su; sannan ya sanya soyayya da rahma a tsakaninku…”
Daga wannan ayar mai albarka, za mu iya fahimtar cewa, natsuwa da juna shi ne farkon tubalin ginin soyayyar auratayya, kuma ma’aurata za su natsu da juna ne kadai in sun kasance sun bi dukkanin dokokin da Allah Madaukaki Ya shar’anta musu game da rayuwa kuma musamman ma game da zamatakewar auratayya, nagartacciyar soyayya mai cakude da tausayi ce za ta biyu, bayan wannan natsuwa. In muka lura, ma’auratan da ba su natsu da juna ba, su ne kullum cikin rikici da rashin kwanciyar hankali da yawan fadace-fadace, in kuwa da su duka za su koma ga Allah gabadaya, su maida al’amarinsu gare Shi, to za su samu natsuwar zuci, wacce a hankali za ta gina masu kamalalliya kuma cikakkiyar soyayya a tsakaninsu. Kamar yadda babban malami Ibnul kayyim ya fada: “Duk wani so da zai janye mutum daga son Allah (rashin yin da’a ga Allah ko saba ma dokokinSa SWT), to azaba ne; Amma son da ya jazar da son Allah shi ne cikakken so, tsarkakakke.”
Soyayya A Sunnar Manzon Allah (SAW)
Haka kuma in muka bibiyi sunnonin Manzon Allah (SAW), za mu samu misalai da yawa kan yadda ake soyayya da yadda ake bayyanar da ita. In mutum yana bin yadda Annabi (SAW) ya yi rayuwar auratayyarsa, zai fahimci cewa Annabi SAW ya kasance kwararre kan wajen iya aikatar da ‘romansiyya’ salo-salo ga matanshi (Radhiyallahu Anhunna –RA), kuma hakan na matukar dadada musu zuciya da kwantar da hankali da cika musu natsuwar zuci. Haka kuma su ma Uwayen Muminai, sun kasance ba su yi kasa da gwiwa ba wajen nuna masa tasu soyayyar. An tambayi Annabi (SAW) wa ya fi so cikin mutane? Ya ce A’ishah (Radhiyallahu Anha –RA); sannan kuma ya ce game da Uwar Muminai Khadija (RA): “Na cika da soyayyar Kha.”
An karbo daga Anas (Radhiyallahu Anhu –RA), cewa Annabi (SAW) ya ce, “Abubuwan da aka soyantar gare ni daga abubuwan wannan duniya su ne mata, turare mai dadin kamshi, kuma sallah ta kasance sanyin idanuwa gare ni.”
Sannan a wani ingantaccen Hadisi, Ibn Abbas (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce: “Ba mu ga wani abu da ya dace ga mutum biyu masoyan juna ba, illa aure.” Watau aure shi ne zai cika soyayyarsu kuma ya inganta ta, amma in ba auren, to soyayyarsu ba za ta amfane su ba, tana ma iya kai su ga sabon Allah Azza wa Jallah.
Soyayya Daga Fahimtar Magabata
Babban Malami Ibnul Jawzee ya yi bayani game da soyayya a cikin littafinsa: Cuta da Magani, cewa: “Yana daga cikin cikar mutumtakar namiji son matan aurenshi, domin Allah Ya albarkaci bayinShi da wannan son, har ma Ya fada, a aya ta 28 cikin Suratul Nisaa’, “Kuma an halicci mutum da rauni (game da mata).” Kuma Manzon Allah ya kasance mai nuna soyayya ga matanshi, haka ma da yawan Annabawan Allah, irin Annabi Ibrahim, Annabi Sulayman, Annabi Dawud (Alaihimus salam –AS) duk sun so matan aurensu”.
Ya kara da cewa, “Son matan aure ko abin da hannun daman mutum ya mallaka (kuyangi) abu ne mai kyau, domin yana kawo alfanu kuma a kan haka ne Allah Ya shar’anta aure don tsare gannai, don haka wannan so ne abin yabawa a wurin Allah, haka kuma a wurin mutane.”
Haka nan Babban Malami Ibn Hazm ya yi gamammen bayani a cikin littafinsa mai suna Zoben Tantara, cewa: “Soyayya ba abin kyama ba ce a addini, ba a kuma haramtata ba a shari’ance, domin kowace zuciya a Hannun Allah take.”
Haka kuma ya kara da cewa, “Ba sha’awa ce kadai soyayya ba, amma dai ita ce masomin soyyayar.”
Sai sati na gaba, in Allah Ya kai mu. Ina fata Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.