Filato: An kafa runduna ta musamman don yaki da ta’addanci

A baya-bayan nan wasu yankuna na Filato sun fuskanci hare-haren ’yan bindiga.

Filato: An kafa runduna ta musamman don yaki da ta’addanci

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kaddamar da wata runduna ta musamman domin yaki da ’yan ta’adda da ke kashe-kashen da lalata dukiyoyin jama’a a Jihar Filato.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun wanda ya ce rundunar ta musamman da Gwamnatin Tarayya ta amince da kaddamarwa a jihohi 10, za ta fara aiki ne nan take a Filato.

Ya sanar da haka ne a lokacin ziyarar da ya kai ƙauyukan jihar Filato domin daɓe wa kansa abin da ya faru a wuraren da aka kai hare-haren.

Tuni dai Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da shiyya ta hudu, Ebong Eyibio ya tura jami’an rundunar ta musamman zuwa yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaro.

A cigaba da neman mafita kan batun kalubalen tsaron, Sanata Filato ta Tsakiya, Diket Plang ya gabatar da wasu batutuwa a gaban Majalisar Dattawa, da ya ce za su taimaka wajen kawo zaman lafiya a jihar.

Sanatan ya koka kan yadda mahara suka ratsa wurare suka mamaye kauyuka fiye da 20 ba tare da wani ya gan su ba.

Ya kuma koka kan yadda wasu ke mamaye gonaki da gidajen wadanda suka yi gudun hijira, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da jami’an tsaro na dindindin a yankunan.

Shi kuwa mai unguwar Dah, Jamok Mafwalal Machambe daga gundumar Butura a Karamar Hukumar Bokkos, ya yi na’am da zuwan jam’an tsaron, sannan ya bukaci jama’a su ba su goyon baya.

Sakataren Kungiyar Miyetti Allah a Karamar Hukumar Barkin Ladi, Abubakar Gambo, ya ce suna bukatar jami’an tsaron su yi adalci.

A makon da ya gabata ne dai mahara suka ka kashe mutane sama da 160 tare da jikkata da dama a wasu yankuna 20 a jihar.