Filato: An sa dokar hana fita ta sa’a 24 a Mangu

An sanya dokar ce sakamakon ci gaban matsalolin tsaro da suka yi ajalalin daruruwan mutane a karamar hukumar Mangu

Filato: An sa dokar hana fita ta sa’a 24 a Mangu

Gwamnan Filato Caleb Muftwang

Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita tsawon awa 24 a Karamar Hukumar Mangu nan take.

Gwamna Caleb Mutfwang ya sanya dokar ce sakamakon ci gaban hare-hare da sauran matsalolin tsaro da suka yi ajalalin daruruwan mutane a karamar hukumar daga karshen shekarar da ta gabata.

Daraktan yada labaran gwamnan, Gyang Bere, ya sanar cewa, “Gwamna Mutfwang ya dauki matakin ne bayan ganawa da hukumomin tsaron da suka dace kuma dokar za ta ci gaba da aiki a karamar hukumar har sai abin da hali ya yi.”

Sanarwar ta umarci jam’a su bi dokar sau da kafa, sannan su ba wa jami’an tsaro hadin kai wajen fallasa bata-gari domin a samu zaman lafiya a karamar hukumar.

Gwamnan ya ba wa al’ummar hakuri bisa takurar da suka shiga a sakamakon dokar, wadda ya ce za a sassauta a lokacin da ya dace.

An dawo da wutar lantarki a Kaduna

An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace