Filato: An shawarci al’umma su guji shan gurbataccen ruwa
Shugaban karamar Hukumar Langtang ta Arewa a Jihar Filato Mista Dan Dul ya shawarci al’ummar karamar hukumar da ta jihar su rika tsabtace muhalli, kuma su guji shan gurbataccen ruwa don kauce wa kamuwa da cututtuka. Shugaban ya shawarci al’ummar ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a ranar Lahadi sakamakon mutuwar […]
Shugaban karamar Hukumar Langtang ta Arewa a Jihar Filato Mista Dan Dul ya shawarci al’ummar karamar hukumar da ta jihar su rika tsabtace muhalli, kuma su guji shan gurbataccen ruwa don kauce wa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ya shawarci al’ummar ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a ranar Lahadi sakamakon mutuwar mutum 10 a yankin Langtang ta Arewa saboda barkewar cutar kwalara.
Shugaban ya ce rashin tsabtace muhalli da shan gurbataccen ruwa kan sa a kamu da cututtukan da za su rika ajalin mutane.
Idan ba a manta ba cutar kwalara ta kashe mutum 10 a kasa da mako daya a karamar hukumar, inda aka kwantar da 48 a asibiti.
Ya ce, “Jami’an lafiya da kuma wani kwamiti na Majalisar Dokokin Jihar sun kawo mana ziyara asibitin da marasa lafiya ke kwance, kuma sun yi alkawarin daukar matakan da suka kamata don hana yaduwar cutar a nan gaba. Ina so al’umma su fahimci cewa, babu abinda zai tafi daidai ba tare da lafiya ba, idan mutum ba ya da lafiya abinci ma ba zai iya ci yadda ya kamata ba, don haka ina ba al’ummata da ta Jihar Filato da ’yan Najeriya shawara su rika tsabtace muhalli, kuma su guji shan gurbataccen ruwa don kauce wa kamuwa da miyagun cututtuka.”