Filato: An yi jana’izar mutum 16 bayan sabon rikici a Mangu
Rikicin dai ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Akalla mutum 16 ne aka yi jana’izarsu biyo bayan wani sabon rikici da ya sake barkewar a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Shugaban Karamar Hukumar kuma Shugaban Kungiyar Agaji ta Jama’atu Nasril Islam (JNI-Aid Group), Malam Jafaru Musa, ya bayyana cewa an yi jana’izar ne a Babban Masallacin Mangu cikin tsaro.
- Abin Da Ya Kamata Ýan Najeriya Su Tambayi Gwamnatin Tinubu
- ECOWAS na yi wa shirin sulhu kafar ungulu — Firaiministan Nijar
Ya ce an birne mamatan ne a makabartar Hayin Layir.
“Mun gano gawarwaki mutum 16 ciki har da jariri.
Mun samu damar birne su a yau (Alhamis) mun yi jana’izarsu gaba daya, muna kuma rokon Allah Ya musu rahama.
“Mutane da yawa sun rasa matsugunansu kuma suna matukar bukatar tallafi. Mutane na bukatar abinci, ruwa, magunguna, tufafi, barguna, tabarmi da katifa.
“Zaman lafiya ya fara samuwa a Mangu saboda muna ganin jami’an tsaro suna zagayawa.”
Shugaban Kungiyar Agaji ta Red Cross a jihar, Nurudeen Husaini Magaji, ya ce sun kafa sansanin ‘yan gudun hijira uku a Mangu, yayin da mutane da dama suka tsere zuwa Bauchi da wasu jihohi.
Aminiya ta ruwaito cewa rikicin Mangu ya fara a ranar Talata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da salwantar gidaje masu tarin yawa.