‘Filato ba za ta bude kasuwar Abuja Market ba saboda dalilan tsaro’
Janar Manajan Hukumar Bunkasa Birnin Jos da Kewaye (JMDB) Birgediya Janar Musa Gambo mai ritaya ya ce Gwamnatin Jihar Filato ba za ta bude kasuwar Abuja Market da sauran shagunan da suke kusa da kasuwar ba har sai bayan wata daya saboda dalilin tsaro.Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya […]

Janar Manajan Hukumar Bunkasa Birnin Jos da Kewaye (JMDB) Birgediya Janar Musa Gambo mai ritaya ya ce Gwamnatin Jihar Filato ba za ta bude kasuwar Abuja Market da sauran shagunan da suke kusa da kasuwar ba har sai bayan wata daya saboda dalilin tsaro.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a Jos a ranar Talata.
An rufe kasuwar Abuja Market wacce ke kusa da Babbar Kasuwar Jos tun bayan tashin tagwayen bama-baman da suka jawo asarar rayuka da dukiya a babbar kasuwar a kwanakin baya.
Gambo ya ce “Dole mutanen da suke kasuwanci a wannan kasuwar su kara hakuri kafin nan da wata daya. Domin sai gwamnati ta yi bincike kan tsaro kafin ta bude kasuwar, baya ga haka wadannan bama-baman da suka tashi sun shafi ginin kasuwar, don haka a yanzu ginin wannan kasuwa ba shi da karfi.”
Ya ce babu yadda za su bar wannan gini ba tare da sun gyara ba.
Ya bukaci ‘yan kasuwar da suka dawo kan hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Jos su tashi.
“Kowa ya san Gwamnatin Jihar Filato ta kafa dokar hana kasa kaya a kan titi a garin Jos da kewaye. Don haka nan ba da dadewa ba za mu fara kama ‘yan kasuwa da suke sayar da kaya a kan titi.
Ya kuma nemi ‘yan kasuwar da ke da shaguna su zauna a cikin shagunansu, kuma kada su bar wani ya rika talla a gaban shagunansu.”
Sai dai ‘yan kasuwar Abuja Market sun musanta cewa ginin kasuwar ya samu wata damuwa, sakamakon tashin bama-baman, sannan suka roki Gwamnatin Jihar Filato ta dubi mawuyacin halin da suke ciki don ta bude musu wannan kasuwa.
Shugaban ‘yan kasuwar Abuja Market Alhaji Sabo Adamu ya ce “Bayanin da Hukumar JMDB ta yi kan cewa ginin kasuwar Abuja Market ya lalace sakamakon tashin bama-baman a kwanakin baya ba gaskiya ba ne. A gaskiya wadannan bama-baman da suka tashi a nesa da kasuwar nan ne suka tashi, kuma babu abin da ya samu ginin wannan kasuwar, babu wani waje da ya nuna alamar rushewa a wannan kasuwa.”
Ya ce sai dai idan gwamnati tana da wata manufa ta daban kan al’amarin.
“Mu ‘yan kasuwar da muke wannan kasuwar, ba mu da matsala da Hukumar JMDB, wadda take da wannan kasuwa, kasancewar muna biyan haraji.”
Ya ce sun kai kukansu ga dukkan inda ya kamata su kai, kan wannan al’amari amma har yanzu babu wanda ya share musu hawaye.
“Tun da aka rufe wannan kasuwa muke cikin wahala, wasu ‘yan kasuwar ko abinci ba su da shi a halin yanzu. Don haka ina fata Gwamnatin Filato za ta tausaya mana ta sake bude mana wannan kasuwa.” Inji shi.