Filato ta samu sabon Kwamishinan ‘yan sandan jihar

An nada Austine Agbonlahor a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato. Agbonlahor zai maye gurbin tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adie Undie, wanda aka sauya wa wrin aiki zuwa hedkwatar ‘yan sandan. Undie, ya rike mukamin ne daga watan Satumba 2017, yayin da kuma aka maye gurbinsa da Ciroma Bala bayan wanin rikici da […]

Filato ta samu sabon Kwamishinan ‘yan sandan jihar

An nada Austine Agbonlahor a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato.

Agbonlahor zai maye gurbin tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adie Undie, wanda aka sauya wa wrin aiki zuwa hedkwatar ‘yan sandan.

Undie, ya rike mukamin ne daga watan Satumba 2017, yayin da kuma aka maye gurbinsa da Ciroma Bala bayan wanin rikici da ya kaure a karamar hukumar Barikin Ladi inda akalla mutum 200 suka rasa rayukansu.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sanda DSP Tyopev Terna ne ya sanar da hakan.