Filato za ta rika tara harajin Naira biliyan daya kowane wata – Mankilik

Shugaban Kwamitin Tara Kudaden Haraji da Gwamnatin Jihar Filato ta kafa, Cif John Mankilik ya ce suna sa ran nan ba da dadewa ba, za su rika tara harajin sama da Naira biliyan daya a kowane wata. Cif John Mankilik ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce […]

Filato za ta rika tara harajin Naira biliyan daya kowane wata – Mankilik

PIC. 23. THE NEW LAMIDO OF ADAMAWA ALHAJI MUHAMMADU BARKINDO ALIYU AFTER HIS INSTALLATION IN YOLA ON THURSDAY (18/3/10).

Cif John MankilikShugaban Kwamitin Tara Kudaden Haraji da Gwamnatin Jihar Filato ta kafa, Cif John Mankilik ya ce suna sa ran nan ba da dadewa ba, za su rika tara harajin sama da Naira biliyan daya a kowane wata.
 Cif John Mankilik ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce a lokacin da aka kafa kwamitin a shekara ta 2011, kudin harajin da suke shiga baitulmalin gwamnatin jihar a wata ba sa wuce Naira miliyan 300 zuwa miliyan 350 Amma sakamakon kafa kwamiti a watan Afrilun da ya gabata sun tara harajin Naira miliyan 877.
Ya ce Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang, ya kafa kwamitin ne ganin cewa bai kamata gwamnatin jihar ta tsaya tana jiran kudin da ake turowa daga Asusun Tarayya ba.  “Don haka Gwamna ya kafa kwamitin domin ya taimaka wa hukumar tara kudin shiga ta jihar,” inji shi.
Cif Mankilik ya ce a kullum suna aiki tsakaninsu da Allah domin sun yi imani cewa idan gwamnati ta samu kudin harajin, za ta yi wa al’umma ayyukan raya kasa, kamar hanyoyin mota da samar da makarantu da asibitoci da ruwan sha.
Ya ce lokacin da suka fara aikin sun gayyaci al’ummomin daban-daban da kamfanoni da hukumomi da masu sana’o’i suka shaida masu cewa ya kamata kowane mutum ya rika biyan haraji.
Ya yi kira ga kananan hukumomin jihar, su duba hanyoyin tattara kudin shiga domin su samu kudin da za su rika gudanar wa al’ummominsu ayyukan raya kasa.
Sai ya yi kira ga al’ummar jihar su taimaki gwamnati wajen biyan haraji, domin da kudin harajin ne gwamnati take gudanar da ayyukan raya kasa.