Filifins ta dasa itatuwa miliyan uku da dubu 300 cikin sa’a guda

Jami’an hukuma a kasar Filifins sun bayyana nasarar da suka samu wajen dashen itatuwa miliyan uku da dubu 300 cikin sa’a guda, a karkashin shirin inganta gandun dazuka. Wannan al’amari ya sanya kasar ke jiran shaidar kambin dashen iatuwa ta duniya daga hukumar kula da kundin tattara bayanai na abubuwan da suka shahara a duniya, […]

Filifins ta dasa itatuwa miliyan uku da dubu 300 cikin sa’a guda
Filifins ta dasa itatuwa miliyan uku da dubu 300 cikin sa’a guda

Jami’an hukuma a kasar Filifins sun bayyana nasarar da suka samu wajen dashen itatuwa miliyan uku da dubu 300 cikin sa’a guda, a karkashin shirin inganta gandun dazuka. Wannan al’amari ya sanya kasar ke jiran shaidar kambin dashen iatuwa ta duniya daga hukumar kula da kundin tattara bayanai na abubuwan da suka shahara a duniya, wato Guiness Book of record.
Za a dan dauki lokaci kafin hukumar kundin Guines Book of Record ta tabbatar wa kasar cewa, ta shiga gaban nasarar da aka taba samu ta dashen itatuwa miliyan daya da dubu 900, a kasar Indiya, ranar 15 ga watan Agustan 2011.
An yi dashen itatuwan ne a yankuna shida na Kudancin tsibirin Mindanao da ke kasar Filifins, inda mutum dubu 160, wadanda suka hada da jami’an gwamanti da dalibai da masu aikin sa kai suka himmatu ka’in da na’in wajen dashen itatuwan, a cewar Daraktan Kula da Muhamma na yankin, Marc Fragada.
“kiddidigar da jami’an mu suka gudanar, ta tabbatar da cewa an dasa itatuwa miliyan uku da dubu 200 a cikin sa’a guda. Har yanzu dai muna tattara bayanai. Dole ne mu tattara shaidu (ga Kundin Guiness),” a cewarsa, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
“An zabo su don masu dashen su kula da su, saboda za su iya zama hanyar neman abincinsu,” inji shi, kamar yadda AFP ya ruwaito.
A cewarsa, Wadannan itatuwa da aka dasa, sun hada da itatuwan da ake kasuwancinsu, irin su Koko da Gahawa da roba.