Fim din batanci: A shirye nake na biya a cire ni —Yakubu Muhammed
Shararren jarumin Kannywood Yakubu Muhammad ya ce a shirye yake ya biya kudi a cire shi daga fim din ‘Fatal Arrogance’ da ake ce-ce-ku-ce a kansa ganin yadda ya yi batanci ga Musulmi musamman ‘yan Shi’a da aka shirya shi a kansu. Yakubu Muhammad ya ce ya yi nadamar rawar da ya taka a fim […]
Shararren jarumin Kannywood Yakubu Muhammad ya ce a shirye yake ya biya kudi a cire shi daga fim din ‘Fatal Arrogance’ da ake ce-ce-ku-ce a kansa ganin yadda ya yi batanci ga Musulmi musamman ‘yan Shi’a da aka shirya shi a kansu.
Yakubu Muhammad ya ce ya yi nadamar rawar da ya taka a fim din.
Ya ce ya shiga fim ne da tunanin a shirya shi ne domin nuna yadda aka musguna wa Musulmi ‘yan Shi’a, amma daga baya ya gano cewa ba manufar fim din ba ke nan.
Tauraron na Kannywood ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa, inda ya ce ya yi kokarin jan hankalin masu shirya fim din kan wasu abubuwa da yake ganin sun saba wa Musulunci tun a lokacin daukar fim din.
- El-Rufai ya ba Kannywood filin gina sinima a Kaduna
- Dalibai sun kirkiri na’urar jinyar masu COVID-19
“Ban taba zaton haka abin zai kasance ba. Na fito a cikin fim din sau shida kacal, inda aka harbe ni, daga baya na mutu.
“Fim ne da ya nuna rikincin da ya auku a tsakanin sojin Najeriya da kungiyar Musulmi mabiya Shi’a a Zariya inda aka kashe ‘yan Shi’a da dama.
“Da na karanta takardar fim din ban ga wani abun suka ga Musulunci a ciki ba ta yadda aka rubuta shi, sai dai ka san sau tari fim na sauyawa daga yadda aka rubuta shi daga fari.
“Na fada wa furodusan fim din ya cire ni daga ciki, kuma a shirye nake na biya su kudin lahanin da wannan mataki nawa zai janyo musu, domin hakan doka ta ce, inji shi.
Ya ce furodusan fim din ya fada masa cewa wata kungiya mai zaman kanta (NGO) ce ta dauki nauyin shirin, kuma a cikin motarsu aka yi ta daukarsa zuwa wajen duakar shirin.
Ya kara da cewa babu wani da ke yi wa rayuwarsa barazana saboda fitowarsa a fim din amma yana ganin yadda ake ta sukar sa da zaginsa a kafafen sada zumunta.
“Akwai wasu wuraren da duk Musulmi idan ya gani dole hankalinsa ya tashi.
“Akwai wani hoto da ke yawo na Mista Pete Edochie sanye da kayan Musulmi tare da wata yarinya yana dauke da kwalbar giya.
“Hakika na yi nadamar fitowa a cikin fim din” inji shi.
Fitaccen jarumin masana’antar fim ta Nollywood, Pete Edochie, ne tauraron fim din mai suna ‘Fatal Arrogance’ wanda Anosike Kingsley Orji ya shirya a garin Inugu a Kudu maso Gabashin Najeriya.
Fim din, al’ummar Musulmi da dama ba su ji dadin yadda aka shirya shi ba, kuma suke fatan kada a fitar da shi.
Hakazalika kungiyar mabiya Shi’a ta IMN sun yi tur da fim din, a sanarwar da ta fitar ta shafin ta na sada zumunta inda ta nuna rashin jindadinta ta yadda aka sanya jagoran mabiya kungiyar Shaikh Ibrahim Zakzaki cikin wata kama mara kyau ta ta’addanci.