Fim din Game of Thrones ya shiga Kundin Tarihi
Fitaccen fim din nan na Game of Thrones ya shiga kundin tarihi na duniya (Guinness Book Of World Records, bayan da aka nuna shi a kasashen duniya 173. Fim din wanda aka rika kuka da wani zubinsa da galibin jarumansa suka mutu shi ne fim mafi girma a ’yan kwanakin nan. Zubinsa na biyar, kashi […]
Fitaccen fim din nan na Game of Thrones ya shiga kundin tarihi na duniya (Guinness Book Of World Records, bayan da aka nuna shi a kasashen duniya 173. Fim din wanda aka rika kuka da wani zubinsa da galibin jarumansa suka mutu shi ne fim mafi girma a ’yan kwanakin nan.
Zubinsa na biyar, kashi na biyu mai suna The House Of Black and White ne aka nuna a kasashe 173 kuma wannan nasarar ce za ta shigar da shi kundin tarihi na duniya a badi.
Jaruma Maisie Williams, wadda ta fito da sunan Arya Stark a zubin fim din ne aka ba ta takrdar shaidar shiga kundin, inda aka ce ta yi niyyar ajiye shi don burge iyayenta.
A baya fim din CSI ne ya fi zama wasan kwaikwayo mafi girma.
A farkon bana nunin fim din ya nuna an samu gagarumar satar fasaharsa, inda kamfanin hana satar fasaha na Irdeto ya gano zubi na daya zuwa na hudu na fim din an kwafe su jim kadan da sake su kafin a sako zubi na biyar.
Shaharar fim din Game Of Thrones ya karu ta yadda mutane suka rika sanya wa ’ya’yansu sunan jaruman fim.
Iyayen jarirai 244 da aka haifa a Ingila da Wales a bara sun sanya wa jariransu sunan Arya, yayin da wasu 53 suka zabi Khaleesi. Sai dai ba wanda ya sanya wa dansa sunan Jon ko Robb ko Jaime a wancan lokacin.