Fim din Krrish 3: Abubuwan da jarumi Hrithik ya fada wajen kaddamarwa
A makon nan ne tawagar ma’aikatan da suka shirya fim din Krrish 3, bisa jagorancin dan wasa Hrithik Roshan ta kaddamar da taba-ka-lashen fim din a birnin Mumbai. Wannan shi ne karo na farko da dan wasan ya bayyana gaban jama’a, tun bayan aikin fida da aka yi masa a kwakwalwa.A yayin kaddamar da samfoton […]

A makon nan ne tawagar ma’aikatan da suka shirya fim din Krrish 3, bisa jagorancin dan wasa Hrithik Roshan ta kaddamar da taba-ka-lashen fim din a birnin Mumbai. Wannan shi ne karo na farko da dan wasan ya bayyana gaban jama’a, tun bayan aikin fida da aka yi masa a kwakwalwa.
A yayin kaddamar da samfoton fim din na Krrish, jarumi Hrithik ya gabatar da wasu muhimman bayanai game da shi kansa, nasararsa da kuma sauran al’amura da suka shafi fim din da sauransu.
Game da aikin fida da aka yi masa a kwakwalwa, Hrithik ya ce: “Duk da cewa na samu laulayi a kwakwalwa, har yanzu ruhina a tsaye yake kuma garau-garau. Babu matsala.” Da wannan bayani ne ya kara tabbatar wa masoyansa cewa zai ci gaba da fantamawa a duniyar fina-finai.
Da ya zo bayani game da kalubalen rayuwa kuwa, Hrithik cewa ya yi: “Babu abin da ya kai inganci da armashi, da ya wuce ka rungumi babban kalubale kasarika, kuma kai tsaye. Kuma babu abin da ya kai dadi, a ce ka samu nasarar cin ma wannan kalubale. Ni na kasance mai kaunar daukar irin wannan mataki.”
Ya kuma yi magana game da shi kansa fim din na Krrish 3, musamman ma wadanda suka sarrafa na’ura a yayin shirya shi. Ga abin da yake cewa: “Wannan fim ne da nake da karancin gudunmowa cikinsa, amma akwai gudumowar mafi yawa daga ma’aikatansa.”
Ya kuma kara da cewa: “Mahaifina ya matsa kaimi cewa dole ne a tsaya nan cikin kasarmu a yi aikin fim din nan, musamman duk siddabarun da ake bukata, a yi shi a nan. Mun yi haka ne domin karfafa wa kwararrunmu na cikin gida gwiwa.”
dan wasan kuma ya bayyana jarumin da yake koyi da shi a fim da kuma dalilinsa na haka. Kamar yadda ya ce: “Dukkan salon da nake zubawa a fim, koyi ne daga Anil Kapoor.” Da haka ne ya ci gaba da cewa, mutane suna ta gaya masa cewa duk al’amuransa na fim suna tuna masu da Anil Kapoor ne. Shi kuwa ya amsa da cewa wannan gaskiya ne, domin da shi yake koyi.