Fim din ‘Ram Leela’ ya haddasa tarzoma a Indiya
Wani fim mai suna ‘Ram Leea’ ya jawo mabiya addinin Kshatriya suka shiga tarzoma a birnin Gujarat, Indiya, inda har suka shiga wani shagon sayar da kayayyaki na zamani suka yi kaca-kaca da shi, musamman saboda an lika fosta-fostar fim din a shagon.Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, fim din, wanda Sanjay Leela Bhansali ya […]

Wani fim mai suna ‘Ram Leea’ ya jawo mabiya addinin Kshatriya suka shiga tarzoma a birnin Gujarat, Indiya, inda har suka shiga wani shagon sayar da kayayyaki na zamani suka yi kaca-kaca da shi, musamman saboda an lika fosta-fostar fim din a shagon.
Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, fim din, wanda Sanjay Leela Bhansali ya shirya kuma ake nufin fitar da shi kasuwa a watan gobe, ya haddasa tarzomar ne a sakamakon yadda suka yi zargin cewa an ci zarafin addinin nasu a cikin fim din.
Masu tarzomar, sun farfasa gilasai da tebura da kujerun shagunan da ke dauke da fostar fim din, sannan kuma suka kona mutum-mutumin furodusan shi. Sun kuma nemi cewa lallai furodusan fim din ya yi hanzarin cire sassan da suke ganin sun ci zarafin addinin nasu daga fim din, kafin ya fitar da shi kasuwa.
A yayin da suke neman a canza tsarin fim din, masu tarzomar sun nemi shi Furodusa Sanjay Leela da ya fito fili ya nemi gafararsu, bisa wannan kuskure da ya yi na cin zarafin addinin nasu.
Kafin wannan tarzoma, an shirya cewa za a fitar da fim din ne a kasuwa, a ranar 15 ga watan gobe, sai dai ganin yadda aka gudanar da zanga-zangar la’antar fim din, akwai yiwuwar a dakatar da fitar da shi a lokacin, domin hana afkuwar wata tarzomar.